Hajiya mai waina ta rabar da wainarta duka albarkacin nasarar Buhari (Hotuna)
Tun bayan samun nasarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi bayan ya sake lashe zaben shugaban kasa daya gudana a karshen makon daya gabata ne jama’a, musamman magoya baya keta bayyana farin cikinsu ta hanyoyi daban daban.
Yayin da wasu suka wuce gona da iri, suka kuma fi mai kora shafawa ta hanyar jefa rayuwarsu cikin hatsari da ma rayuwar wasu da sunan suna murnar samun nasarar Buhari, wasu kuma murna suka yi mai tsafta, suka kuma amfanar da wasu.
KU KARANTA: Kaico! An kashe na’ibin limamin Masallaci a yayin murnar nasarar Buhari
Anan ma wata mata mai sana’ar sayar da waina wanda wasu ke kira masa, Hajuya Sakina Muhammad Basawa ce ta rabar da wainar da ta toya kyauta ga jama’a, albarcin nasarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu.
Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, Sani Bala Yauri ne ya tabbatar da hakan, inda yace lamarin ya faru ne a garin Yauri ta jahar Kebbi, inda yace Hajiya Sakina mai waina ta rabar da wainar ne a rumfar sana’arta dake Yabo, gab da barikin Yansanda.
Idan za’a tuna, a jawabinsa na farko tun bayan lashe zabe, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga magoya bayansa da kada su wuce gona da iri wajen murnar zabe ko kuma su jefa kansu cikin hadari da sunan murna.
Sai dai ba dukkanin magoya bayan nasa bane suka dauki maganar da yayi kamar yadda Hajiya Sakina tayi ba, inda wasu suka kashe kansu, suka kashe wasu, suka jefa rayuwarsu cikin hadari tare da yin barazana ga rayuwar wasu duk da sunan murna.
Legit.ng ta ruwaito wani na’ibin Limami ne a jahar Adamawa ya rasa ransa sakamakon irin wannan mummunan halayya ta wasa da ababen hawa da wasu jama’a suka nuna wai da sunan suna murnar samun nasarar da Buhari ya samu a zaben shugaban kasa.
Wannan lamari ya faru ne a garin Mubi, a lokacin hatsari ya rutsa da Malam Adamu, dattijon arziki kuma na’ibin limami a masallacin rukunin gidaje na Shuwarin, yayin da yake kokarin tsallaka titi a ranar Talata.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng