Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta sake kama masu shaye-shaye

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta sake kama masu shaye-shaye

- NDLEA ta kama matasa 36 wanda ya hada har da mata bisa laifin shaye shaye

- Gaba daya wadanda aka kama din basu wuce shekaru 14 zuwa 25 ba

- An fara kama mutane 25 kafin a shiga satin zabe yayin da aka kama ragowar 11 kwana hudu dayin zabe

Zabe: Bai kamata a bari APC
Zabe: Bai kamata a bari APC
Asali: UGC

An kama matasa 36 wanda ya hada da mata guda Uku bisa laifin shaye-shaye,an samu nasarar kamasu ne a cikin makwanni Biyu kawai a Kwara.

Mr Ona Ogilegwu kwamandan NDLEA na jihar ne ya bayyana hakan.

"Mun kama yan shaye- shaye 25 kafin satin zabe sannan muka kara kama 11 bayan kwanaki Hudu da yin zabe,mun kamasu a mabanbanta wurare wanda ya hada da Asadam,garejin mota na Maraba, Idiape da kuma Oko-olowo".

GA WANNAN: Yaki na iya barkewa tsakanin kasashen Indiya da Pakistan, kasashe masu makaman Nukiliya

"Sannan muna kokarin bawa masu tu'ammali da wiwi shawara su kuma dilolin muna mikasu hannu hukuma".

Wadanda aka kama basu wuce shekara 14 zuwa 25 ba.

Shugaban na NDLEA ya kara da cewa mafi yawan wadanda aka kamadin suna tu'ammali da wiwi da Tramadol.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel