Yaki da rashawa: Sabbin Sanatoci 12 da zasu shiga majalisa tare da guntun kashi a gindinsu

Yaki da rashawa: Sabbin Sanatoci 12 da zasu shiga majalisa tare da guntun kashi a gindinsu

An yi zabe an gama, sai dai don gudun kada ayi tuya a manta da albasa yasa muka dauko bayanai dangane da yadda zaman majalisar dattawa ta Tara za ta kasance duba da cewa akwai sababbin Sanatoci da suka lashe zabe amma suke da matsala da EFCC.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin sababbin Sanatocin da zasu angwance da majalisar dattawa bana akwai Sanatoci goma sha daya da suke fuskantar tuhume tuhumen cin hanci da rashawa da dama daga hukumar EFCC.

KU KARANTA: Daga fadar gwamnati zuwa majalisar dattawa: Jerin wasu gwamnoni guda 6 da kakarsu ta yanke saka

Daga cikin Sanatocin nan akwai

Orji Uzor Kalu: Tsohon gwamnan jahar Abia daga shekarar 1999 zuwa 2007, wanda ya lashe zaben Sanatan mazabar Abia ta Arewa a inuwar jam’iyyar APC, da a yanzu haka EFCC ke tuhumarsa da laifin satar naira biliyan bakwai da miliyan dari bakwai (N7.7bn) a zamanin yana gwamna.

Gabriel Suswam: Tsohon gwamnan jahar Benuwe daga shekarar 2007 zuwa 2015, wanda ya lashe zaben Sanatan mazabar Benuwe ta Arewa a inuwar jam’iyyar PDP, da a yanzu haka EFCC ke tuhumarsa da laifin satar naira biliyan tara da miliyan dari bakwai (N9.7bn) a zamanin yana gwamna.

Ibrahim Shekarau: Tsohon gwamnan jahar Kano, wanda ya lashe zaben Sanatan mazabar Kano ta tsakiya a inuwar jam’iyyar APC, da a yanzu haka EFCC ke tuhumarsa da laifin handame naira miliyan dari tara da hamsin (N950m) kudin makamai a zamanin Jonathan.

Chimaroke Nnamani: Tsohon gwamnan jahar Enugu daga shekarar 1999 zuwa 2007, wanda ya lashe zaben Sanatan mazabar Enugu ta gabas a inuwar jam’iyyar PDP, da a yanzu haka EFCC ke tuhumarsa da laifin satar naira biliyan biyar da miliyan dari uku (N5.5bn) a zamanin yana gwamna.

Ifeanyi Ubah: Hamshakin dan kasuwa daya lashe zaben Sanatan mazabar Anambra ta kudu a inuwar jam’iyyar YPP. Sai dai shima EFCC na tuhumarsa tare da kamfanin Capital Oil and Gas Ltd da laifin almundahanar kudin tallafin man fetir na naira biliyan 43.29.

Peter Nwaoboshi: Mista Peter ya samu nasarar komawa mukaminsa na Sanata mai wakiltar Delta ta Arewa a majalisar dattawa a inuwar jam’iyyar PDP, sai dai shima EFCC na tuhumarsa da badakalar rashawan naira miliyan 322.

Abba Moro: Tsohon ministan cikin gida a zamanin Goodluck Jonathan, wanda ya lashe zaben Sanatan mazabar Benuwe ta Arewa a inuwar jam’iyyar PDP, da a yanzu haka EFCC ke tuhumarsa da laifin satar dala miliyan 2.5.

Stella Oduah: Tsohuwar ministar sufurin jirgin sama a zamanin Goodluck Jonathan, wanda ta sake lashe zaben Sanatan mazabar Anambra ta Arewa a inuwar jam’iyyar APGA, da a yanzu haka EFCC ke tuhumarta da laifin satar dala biliyan 3.9.

Ike Ekweremadu: Mataimakin shugaban majalisar dattawa, wanda ya sake lashe zabe a karo na biyar don don wakiltar mazabar Enugu ta yamma a majalisar dattawa wanda EFCC ke tuhumarsa da mallakan gidaje 22 a Abuja, Landan, Amurka da Dubai.

Danjuma Goje: Tsohon gwamnan jahar Gombe, wanda ya sake lashe zaben Sanatan mazabar Gombe ta tsakiya a inuwar jam’iyyar APC, da a yanzu haka EFCC ke tuhumarsa da laifin satar naira biliyan 25 a zamanin yana gwamna.

Abdullahi Adamu: Tsohon gwamnan jahar Nassarawa, wanda ya lashe zaben Sanatan mazabar Nassarawa ta yamma a inuwar jam’iyyar APC, da a yanzu haka EFCC ke tuhumarsa da laifin satar naira biliyan 15 a zamanin yana gwamna.

Aliyu Magatakarda Wammako: Tsohon gwamnan jahar Sakkwato, wanda ya lashe zaben Sanatan mazabar Sakkwato ta Arewa a inuwar jam’iyyar APC, da a yanzu haka EFCC ke tuhumarsa da laifin satar naira biliyan goma sha biyar (N15bn) a zamanin yana gwamna.

Dino Melaye: Sanatan dake wakiltar mazabar Kogi ta yamma wanda ya sake lashe zabensa a inuwar jam’iyyar PDP, sai dai babu mai tuhumarsa da satar kudin jama’a, amma fa akwai tuhme tuhume akansa daga rundunar Yansandan Najeriya daya hada da zargin kashe jami’in Dansanda Danjuma Saliu a garin Lokoja.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel