Murnar samun nasara: Wani Soja ya dirka ma magoya bayan Buhari bindiga a Adamawa

Murnar samun nasara: Wani Soja ya dirka ma magoya bayan Buhari bindiga a Adamawa

Wani rahoto mai tayar da hankali ya bayyana yadda wani jami’in rundunar Sojan Najeriya ya kusa halaka wasu magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin da suke bayyana farin ciki tare da murnar samun nasarar da yayi a zaben daya gabata.

Wannan lamari ya faru ne a garin Numan na jahar Adamawa, kamar yadda wani ma’abocin kafar sadarwar zamani na Facebook, kuma shugaban JIBWIS Social Media, Abdulrashin Yahaya ya bayyana a shafinsa.

KU KARANTA: Yan bindiga sun bude ma magoya bayan Buhari wuta yayin da suke tsaka da murnar nasara

Murnar samun nasara: Wani Soja ya dirka ma magoya bayan Buhari bindiga a Adamawa
Wani Soja ya dirka ma magoya bayan Buhari bindiga a Adamawa
Asali: Facebook

Majiyan Legit.ng ya bayyana cewa a ranar Laraba, 27 ga watan Feburairu ne jama’an Musulmai suka fito manyansu da kananansu suna murnar samun nasarar Buhari sai kwatsam wasu gungun matasan kabilar Bwatiye suka kai musu farmaki da nufin hanasu murnar da suke yi.

Sai dai ba’a kai ga kacamewa ba sai dakarun Sojin Najeriya suka bayyana da nufin kwantar da tarzomar dake neman tashi, amma sai wasu matasan Bwatiye suka shiga jifansu, wanda hakan ya harzuka Sojoji suka kamasu tare da jibgarsu.

Ana cikin haka ne sai wani jami’in Soja ya karkata zuwa kan Musulman dake gefe guda ya bude musu wuta, a sanadiyyar haka mutane biyar suka samu rauni, daga cikinsu har da wani karamin yaro.

Daga cikin wadanda harbin ya shafa akwai Abba Dan Kano, Yakubu Ibrahim, Mubarak Ahmad, Aisha Umar Peta da Kabiru Alpha, a yanzu haka dukkaninsu suna asibitin Grace Land Specialist suna samun kulawa.

A daya hannun kuma, wasu gungun yan bindiga a ranar Laraba 27 ga watan Feburairu sun bude ma taron masoya shugaban kasa Muhammadu Buhari wuta yayin da suka tsaka da bikin murnar samun nasarar da Buhari yayi a zaben shugaban kasa.

Wannan lamari mai matukar muni ya faru ne a daidai layin Iyawa a unguwar Sabo dake yankin Yaba na jahar Legas, inda yan bindigan suka tarwatsa taron magoya bayan Buharin bayan sun bude musu wuta, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel