Yaki na iya barkewa tsakanin kasashen Indiya da Pakistan, kasashe masu makaman Nukiliya

Yaki na iya barkewa tsakanin kasashen Indiya da Pakistan, kasashe masu makaman Nukiliya

- Kasashen Indiya da Pakistan basu ga maciji da juna

- Suna ta kaima juna hari kan Kashmir

- Duniya tayi kira dasu zauna da juna lafiya

Akalla mutum 30 'yan PDP ne suka rasu a hadurruka daban-daban a yau
Akalla mutum 30 'yan PDP ne suka rasu a hadurruka daban-daban a yau
Asali: Facebook

Ana tsoron sabon fada na iya barkewa tsakanin kasashen Indiya da Pakista, kasashe Hassan da Usaini masu baqar gaba da juna.

Rigimarsu dai ta faro ne tun zamanin sahabbai, bayan da Musulmi suka musuluntar da bangaren kasar daga yamma, suka hana bautar gunki.

A zamanin mulkin Turawa sai aka raba kasar, Musulmi suka dau rabi, Hindu suka dau rabi, sai dai akwai wurare masu arziki da Indiya taki barwa PAkistan, domin kuwa koda 'yan garin musulmi ne, tarihi da arzikin yankin yafi alaka da Indiya.

GA WANNAN: Jamiyyar APC tayi babban rashi bayan da aka kada Sanatan ta a jihar sa ta Benue

Yanzu dai, kasashen suk suna da makaman Nukiliya, kuma sun ki yarda su so juna, duk da kakanninsu daya, yaronsu daya, al'adunsu daya.

Sabon yakin da ka iya kazancewa, na cacan baka ne kan Kashmir, yanzu ya fara daukar sabon salo, bayan da kasashen suka fara kutse cikin kasashen juna da jirragen yaki su kuma sojinsu ke kakkabo su.

A wannan yanayi dai, duniya tace su zauna a teburin sulhu, amma saboda akwai zabuka masu karatowa a Indiya, babu alamar za'a sauke jijiyar tukun, sai azarbabi ake kan juna.

Hari ne dai aka kai wa sojin Indiya a wannan watan, wanda ya hallaka sojinta 40, aka kuma gano masu aikin jihadi ne suka kai shi kan 'yanto Musulmin Kashmir daga Mulkin Indiya, wanda aka jima ana yakin a kai.

Indiya tace zata rama, sai dai kan kasar da ke baiwa su 'yan ta'addar mafaka a zarginta zata rama. Pakistan tace bata ajje masu tada kayar baya, kuma duk wani hari zasu kakkabe shi kuma su rama. Dukkan kasashen suna da muggan makamai na Nukiliya masu kisan kare-dangi kaf!

Yariman Saudiyya ma dai, mai jiran gado MBS, a ziyararsa ta makon jiya, ga kasashen biyu, yayi kira da a zauna ayi sulhu, a mutumta juna, bayan da yayi alkawarin zuba jari a kasashen, mai dumbin yawa.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel