Ihu bayan hari: A jihar Delta, APC na kukan a soke zaben shugaban kasa da na majalisu na jihar

Ihu bayan hari: A jihar Delta, APC na kukan a soke zaben shugaban kasa da na majalisu na jihar

- Anyi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta da ta dau mataki akan zaben jihar Delta

- Akwai yakunan da ba'ayi zaben ba, ballantana yankunan ruwa

- Hakan barazana ce ga damokaradiyyar mu kuma akwai fayafayan bidiyo da zasu zama shaida akan hakan

A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka
A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka
Asali: Depositphotos

Jam'iyyar APC reshen jihar Delta ta zargi magudi mai yawa a zaben shugaban kasa da majalisar dattawa da akayi a ranar asabar. Jam'iyyar ta zargi shuwagabannin jam'iyyar PDP da jan hankalin jami'an hukumar zabe mai zaman kanta da jami'an tsaro wajen yin damfarar zabe.

Jam'iyyar tayi alkawarin sakin hotuna da fayafayan bidiyo da zai zamo shaida ga abinda ta fada.

Jam'iyyar ta fadi hakan ne a wata takarda da taba manema labarai watch shugaban kamfen dinta na jihar Delta Hon. Timinimi George yasa hannu a ranar talata.

A don haka ne jam'iyyar tayi kira da a soke sakamakon kananan hukumomin da abin ya shafa.

"Ba a yi zabe ba a yankuna masu ruwa a Delta ta kudu. Abinda ya faru shine fashin tsakar rana kuma abin kunya ga damokaradiyyar mu. Shuwagabannin PDP a jihar sun tankwasa sojoji da yan sandan da aka tura don tabbatar da anyi zaben gaskiya. A Delta Delta ta kudu, guraren ruwa na Burutu, Bomadi da Patani, shuwagabannin sun kwace takardun zabe inda suka dinga dangwale,"

Jam'iyar tana zargin jagoran jam'iyar ta PDP a jihar yayi hadin baki da jami'an hukumar zabe da kuma jami'an tsaro wajen yin magudi a zaben.

Jam'iyar tayi alkawarin bayyana shaidar ta na cewa anyi magudin ta hanyar hotuna da kuma bidiyo.

Jam'iyar ta bayyanawa manema labarai hakan ne ta bakin darakta Janar (DG) Hon. Timinimi George a ranar Talata.

Jam'iyar tayi kira da a soke zaben kananan hukumomin da suka samu tangarda.

"Wuraren dake kusa da ruwa a kudancin jihar Delta basu da zabe duba a abun da ya faru a na fashi da tsakar rana wanda ya zamto abin kunya a dimukradiyyar mu".

A kudancin jihar ta Delta wanda ya hada da Burutu,Bomadi,da kuma karamar hukumar Patani shugabannin jam'iyar PDP sunyi satar takaddun zabe inda suka tafi suka dangwala hannu.

GA WANNAN: INEC ta soke zaben mutum 55,000 saboda injin tantance katin masu zabe

"Inda sukayi dangwalen babban gurine inda mata da maza suka dinga aikin ta'addancin nan. Ina da faifan bidiyo da zai tabbatar da abinda nake cewa," inji George.

Da yayi magana akan takamaiman guraren da abin ya shafa, DG din yace: "A yankin Ogbe-Ijoh na Warri ta kudu maso yamma, gunduma ta daya, akwatin na 5, 6, 7 da 8 yankunan ruwa, babu zaben da akayi. Sun hada baki ne da ma'aikatan inda suka tafka magudi son ransu. Akwai hancina, daba da tsorata masu jefa Kuri'a da wakilan jam'iyyu.

Anyi hakan ma a Gbaramatu, Oporoza da Isaba. Kananan hukumomin Burutu da Bomadi, karamar hukumar Patani ma duk sunyi haka ne. Abin haushi ma acikin guraren da sukayi magudin, an sace takardar rubuta sakamakon zabe. A don haka ne nake kira ga hukumar zabe mai zaman kanta da ta dau mataki akan hakan domin barazan ce babba ga damokaradiyyar mu."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel