Ban yarda da sakamakon zabe ba - Atiku

Ban yarda da sakamakon zabe ba - Atiku

Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ba zai aminta ba da sakamakon babban zaben kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu 2019. Ya ce zaben cike yake da murdiya gami da rashin gaskiya.

Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyar PDP, ya ce ba zai taba amincewa da sakamakon babban zaben kasa da hukumar INEC ta bayyana a yau Laraba, 27 ga watan Fabrairun 2019.

Ban yarda da sakamakon zabe ba - Atiku
Ban yarda da sakamakon zabe ba - Atiku
Asali: Twitter

A sakamakon zaben da hukumar INEC ta bayar da shaida ta bayyana cewa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari, ya yi nasara a yayin babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019.

Tsohon Mataimakin shugaban kasar cikin jawaban sa ya bayyana cewa, babban zaben kasa da hukumar INEC ta gudanar a makon da ya gabata cike yake da murdiya, magudi gami da duk wani nau'i na rashin adalci da rashin gaskiya.

A sanadiyar haka, Wazirin Adamawa ya ce zai nemi hakkin sa gaban Kotu da ba bu shakka a halin yanzu ya shirya tsaf wajen garzaya wa da koken sa. Ya ce ba zai taya shugaban kasa Buhari murna ba kasancewar rashin gaskiya da ta yi kaka-gida yayin gudanar zaben.

KARANTA KUMA: Nasarar Buhari alama ce ta nasarar Dimokuradiya - Mijinyawa

Cikin jawaban sa, Atiku bayan jinjina ga al'ummar kasar nan da suka yi tururuwa wajen jefa kuri'u domin tabbatar da 'yanci su. Sai dai ya ce yiwa dimokuradiyya karan tsaye ta hanyar rashin gaskiya da mugudi da ba zai lamunta ba sun auku musamman a jihohin Akwa Ibom, Legas, Ribas, Imo, da kuma jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya da ta'addanci Boko Haram ya mamaye.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel