2019: An fito da sakamakon zaben Jihar Sokoto da kuma Jigawa

2019: An fito da sakamakon zaben Jihar Sokoto da kuma Jigawa

Yanzu haka dai sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a karshen makon jiya yana cigaba da bayyana. Mun ji labari cewa shugaba Muhammadu Buhari ya sake samun nasara a wasu jihohi da ke cikin Arewa.

2019: An fito da sakamakon zaben Jihar Sokoto da kuma Jigawa
Atiku ya sha kasa a hannnun Buhari a Jigawa da Sokoto
Asali: Twitter

Sakamakon da mu ka samu daga jihar Jigawa ya nuna cewa jam’iyyar APC mai mulki ce tayi nasara. Jam’iyyar ta samu kuri’a 794, 737 ne yayin da ‘Dan takarar jam’iyyar PDP mai adawa, Atiku Abubakar ya zo na biyu a zaben.

Alhaji Atiku Abubakar ya samu kuri’a 289, 297 ne a jihar Jigawa kamar yadda sakamakon zaben da mu ka samu ya bayyana. Sai dai har yanzu hukumar zabe mai zaman kan-ta na INEC ba ta tabbatar da wannan sakamako ba.

KU KARANTA: Atiku Abubakar ta ji babu dadi a hannun APC a Jihar Shugaban kasa

A jihar Sokoto kuma shugaba Muhammadu Buhari ne yayi nasara bayan an tattara sakamakon duka kananan hukumomin jihar 23 da ake da su. Jam’iyyar APC ta samu kuri’a 490, 333 inji ita kan-ta hukumar zabe watau INEC.

Malamin zaben da yayi aiki a jihar Sokoto, Farfesa Muhammad Yahuza ya bayyana cewa PDP Ta samu kuri’a 361, 604 a jihar. Atiku dai ya samu sama da kashi 40% na kuri’ar da aka kada a jihar Sokoto wanda hakan ya bada mamaki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel