Kakakin Majalisar Kano ya lashe Kujerar Majalisar Tarayya

Kakakin Majalisar Kano ya lashe Kujerar Majalisar Tarayya

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta tabbatar da nasarar Alhaji Kabiru Alhassan, kakakin majalisar dokoki ta jihar Kano, a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar majalisar wakilai ta kananan hukumomin Rano, Bunkure da Kibiya.

Babban Alkali zaben na jihar Kano, Farfesa Kabir Tahir-Hamid, shine ya bayar da wannan sanarwa a yau Litinin cikin babban birni na Kanon Dabo a wata hira yayin ganawa da manema labarai.

Kakakin Majalisar Kano ya lashe Kujerar Majalisar Tarayya
Kakakin Majalisar Kano ya lashe Kujerar Majalisar Tarayya
Asali: Depositphotos

A cewar sa, Alhaji Kabir Alhassan, dan takarar na jam iyyar APC, ya samu nasara da kimanin kuri'u 62,455 inda ya samu damar tserewa abokin takarar sa na jam iyyar PDP, Alhaji Sani Muhammad, wanda ya samu kuri'u 33,296 kacal.

Kamar yadda Farfesa Hamid ya bayyana, dan takarar kujerar Majalisar wakilan ya samu gamayyar kuri u 62,455, inda Alhaji Sani Muhammad ya samu gamayyar kuri'u 33,296 bayan kammala kidaya ta tantance kuri'un da aka kada.

KARANTA KUMA: Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno

Fashin bakin na nuna cewa, Alhassan ya samu kuri'u 16,505 a karamar hukumar Kibiya, yayain da abokin takarar sa, Muhammad, ya samu kuri'u 2,543.

A karamar hukumar Rano, Alhassan ya lashe kuri'u 21,459, yayin da Muhammad ya samu kuri'u 9,292. Sai kuma karamar hukumar Bunkure inda Alhassan ya samu 24,491 yayin da Muhammad ya samu kuri'u 11,461.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel