Zaben 2019: Shugaba Buhari ya lallasa Atiku a kananan hukumomi 11 na jihar Kano

Zaben 2019: Shugaba Buhari ya lallasa Atiku a kananan hukumomi 11 na jihar Kano

Rahotanni da ke zuwa mana a yanzu sun tabbatar da cewa, dan takarar kujerar shugaban kaa na jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari, ya yiwa babban abokin adawar sa shigar wuri, dan takara na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a jihar Kano.

A yayin da sakamakon babban zaben da aka gudanar a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairun 2019, ya fara bayyana, mun samu cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa tsohon mataimakin shugaban kasa shigar wuri cikin kananan hukumomi 11 na jihar Kano.

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu cewa, shugaban kasa Buhari ya yiwa Wazirin Adamawa wucin kece raini yayin da hukumar zabe ta kasa wato INEC ta bayyana sakamakon babban zaben wasu kananan hukumomi 11 na jihar Kano.

Zaben 2019: Shugaba Buhari ya lallasa Atiku a kananan hukumomi 11 na jihar Kano
Zaben 2019: Shugaba Buhari ya lallasa Atiku a kananan hukumomi 11 na jihar Kano
Asali: UGC

Shugaban kasa Buhari ya lashe kuri'u 26,110 cikin karamar hukumar Madobi yayin Atiku ya samu kuri'u 13,113 kacal. Buhari ya kuma lashe kuri'u 24,420 yayin da Atiku ya samu kuri'u 6,130 a karamar hukumar Gabasawa.

A karamar hukumar Rimin Gado kuma, Atiku ya samu kuri'u 10,305 yayin da Buhari ya kere sa da kuri'u 20,582. Buhari mai kuri'u 23,375 ya yiwa Atiku nisa mai kuri'u 10,584 a karamar hukumar Bagwai.

Cikin karamar hukumar Bunkure kuma, Buhari samu kuri'u 27,232 yayin da Atiku ya lashe kuri'u 9,528 kacal. Sakamakon zaben karamar hukumar Tofa ya bayyana yadda Buhari ya samu kuri'u 19,984 yayin da Atiku ya kwashi kuri'u 7,732.

KARANTA KUMA: Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno

Daga karamar hukumar Garun Mallam kuma, Buhari ya lashe kuri'u 23,810 yayin da Atiku ya tsira da kuri'u 4,861 kacal. Buhari ya kuma lashe kuri'u 37,147 yayin da Atiku ya samu kuri'u 6,507 kacal a karamar hukumar Dawakin Tofa.

A yayin da alkalan zabe ke ci gaba da tatancewa tare da kidayar kuri'u, majiyar rahoton ta bayyana cewa, shugaban kasa Buhari ya yiwa Atiku nisan da ba zai ji kira ba yayin da sakamakon kananan hukumomin Kura, Karaye da kuma Kibiya suka bayyana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel