Zaben 2019: An tattara sakamakon zabe daga Kananan hukumomi 13 na Jihar Kaduna
Mun sake samun sakamakon zaben shugaban kasa daga jihar Kaduna bayan kananan hukumomin da aka fitar a baya. Yanzu INEC ta bayyana cewa Atiku Abubakar yayi nasara a kananan hukumomi 5.
An sanar da cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ne yake jan ragamar kuri’un yankin inda ya samu nasara a kananan hukumomi irin su Ikara, Makarfi, Kudan, Kubau Giwa, Sabon Gari, Soba, da kuma Kauru.
Ga sakamakon zaben yankin nan kamar haka:
Kauru
APC 33, 578
PDP 27,041
Kagarko
APC 16,663
PDP 21,605
Kajuru
APC 7,888
PDP 31,445
Giwa
APC 45,574
PDP 9,838
KU KARANTA: Jam’iyyar PDP ta ji babu dadi a hannun APC a Jihar Katsina
A baya dai kun ji labarin yadda zaben ya kaya a sauran kananan hukumomin jihar da su ka hada da:
Kaura
APC 6,907
PDP 33,647
Ikara
APC 44,021
PDP 14,464
Makarfi
APC: 36,624
PDP:14,494
Kubau
APC: 67,140
PDP: 13,296
KUDAN
APC:30,577
PDP: 11,692
JABA
APC:6,400
PDP:22, 758
Zangon Kataf
APC:10,411
PDP:62,622
Sabon Gari
APC 58,467
PDP 22,644
SOBA
APC 51, 548
PDP 10, 656
KU KARANTA: Danjuma La’ah ya doke Bala Bentex a akwatin cikin Garin Manchok
Mun kuma samu labarin kujerun majalisar tarayya a bangarorin jihar inda Jam'iyyar APC ta ci kujerar Majalisar Soba da kuri'a 30, 398, ita kuma PDP ta samu 14, 382. Hamza Ibrahim ne ya samu galaba a kan Khalid Ibrahim na PDP.
Haka kuma mun ji cewa PDP ta rasa kujerar Majalisar Tarayyar Makarfi a Kaduna. Atiku ya sha kasa ne a yankin tsohon shugaban PDP Ahmad Makarfi inda Sani Shehu Ladan na APC ya doke Ahmed Hassan Jumare a kujerar majalisa.
Dazu nan mu ka ji cewa jam'iyyar APC ta sake samun kujerar majalisar tarayya a Yankin Ikara da Kubau da ke cikin jihar ta Kaduna. APC ta samu kuri'a har 101, 364 inda shi kuma 'dan takarar PDP mai adawa ya samu kuri'a 35, 956.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng