Cin amana: An kama wani sufeton 'yan sanda na taimakawa 'yan daba yin basaja

Cin amana: An kama wani sufeton 'yan sanda na taimakawa 'yan daba yin basaja

An kama wani jami'in dan sanda mai mukamin sufeta a ranar Alhamis a wani Otel da ke rukunin gidaje na Ewet da ke Oyo a jihar Akwa Ibom da aka samu yana taimakon wasu mutane yiwa wasu motocci fainti irin na motoccin 'yan sanda da bata gari za suyi amfani da su a ranar Asabar da za a gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya.

Punch ta gano cewa motocci biyun kirar Volvo V70 suna daga cikin irin motocin da gwamnatin jihar ta sayo wa 'yan sanda reshen jihar da ayi amfani da su saboda aikata magudin zabe.

Wata majiya mai masaniya a kan lamarin ta ce 'yan sandan sun gano 'yan daban siyasar da dan sandan ne a wani Otel yayin da suke yiwa motoccin fainti irin na motoccin 'yan sanda.

Cin amana: An kama wani sufeton 'yan sanda na taimakawa 'yan daba yin basaja

Cin amana: An kama wani sufeton 'yan sanda na taimakawa 'yan daba yin basaja
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Wasu na kusa da Buhari za su taimakawa Atiku samun nasara - PDP

Ya ce, "An samu bayanin cewa wasu 'yan daban siyasa suna yiwa wasu motocci kirar Volvo V70 irin na wanda gwamnatin jihar ta bawa 'yan sanda.

"Har an riga an sanya wa motoccin jiniya da tambarin rundunar 'yan sanda da lambobi.

"A yayin da 'yan sanda suka isa Otel din, wadanda ake zargin sun riga sun gudu da mota guda yayin da sauran daya kuma an yi mata fainti tare da taimakon wani jami'in dan sanda mai mukamin mataimakin sufeta.

"An tafi da sufetan dan sandan zuwa caji ofis kuma an kwace motar.

"Wanda aka kama ya bayar da wasu bayanai masu muhimmanci har ya fadi sunayen wadanda suka sanya shi aikin.

Ana cigaba da gudanar da bincike, Sufeta 'yan sandan yana aiki ne da sashin tattara bayanan sirri da rundunar 'yan sanda a jihar Akwa Ibom.

Da aka tuntube shi, Kakakin 'yan sanda na jihar Mr Odiko MacDon ya ce a halin yanzu bai da masaniya akan labarin amma ya ce idan ya kasance gaskiya ne tabbas doka za tayi aikinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel