Jihohin dake da katin zabe mafi yawa su zasu nuna wanda zai lashe zaben jibi

Jihohin dake da katin zabe mafi yawa su zasu nuna wanda zai lashe zaben jibi

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta fitar da kiyasin jihohi masu yawan katikan zabe

- Jihohi hudu ne akan gaba kuma jihohin na Karkashin APC ne

- Yankin Kudu maso gabas ne koma baya duk da an samu gobar a wasu ofisoshin hukumar na yankin

Jihohin dake da katin zabe mafi yawa su zasu nuna wanda zai lashe zaben jibi

Jihohin dake da katin zabe mafi yawa su zasu nuna wanda zai lashe zaben jibi
Source: UGC

A ranar alhamis ne hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana jimillar yawan katin zabe na dindindin da aka karba kafin ranar asabar ta zaben shugabancin kasa.

A ranar Fabrairu 11 ga wata, an karba katin zabe miliyan 72.8 a fadin kasar nan, inda jihar Legas da Kano ke kan gaba.

Shugaban hukumar, Mahmood Yakubu, ya bayyana hakan yayi jawabi a Abuja.

Jihar Legas dake kan gaba an karba katin miliyan 5.5. Kano ke binta da katika miliyan 4.7.

Legas da Kano na biye ne da Kaduna, Katsina da jihar Rivers. Kaduna na da katika miliyan 3.6 , Katsina na da katika miliyan 3.2 sai jihar Rivers dake da miliyan 2.83.

Jihohi masu karantar karbar katikan sune Ebonyi, Bayelsa da Kwara.

Jimillar katikan zaben na dindindin da aka karba a kowace jiha na nuna yawan kuri'un da kowacce jiha zata kawo.

Amma kuma sakamakon zaben da ya gabata ya nuna cewa samun yawan katikan zabe a jiha ba shine ke nuna yawan mutanen da zasu kada kuri'a ba balle ma akwai mutanen dake karbar katin kuma su ki zuwa kada kuri'a.

Jihohi hudu da suke jagoranta a yawan katikan zaben sune kuma jihohin da yan kiyasin siyasa kesa ran zasu zama bakin fama a zabe mai zuwa.

GA WANNAN: Sakataren PDP na jihar Uzor Kalu ya ajje aikinsa ana tsaka da tsare-tsaren cin zabe

Jihohi hudun kuma na karkashin ikon jam'iyya mai mulki ta APC ne. Baya da gwamna Akinwumi Ambode na jihar Legas, sauran gwamnoni ukun na jihohin da suka fi yawan katikan zaben nason komawa kujerun su.

Jihar Katsina kuwa itace jihar shugaban kasa Muhammadu Buhari wacce tafi kowacce jiha yawan mutanen da suka karbi katin zaben su na dindindin.

Idan kuma muka dubi yankuna 6 na kasar nan, zamu gano cewa arewa maso yamma ce ke kan gaba wajen yawan mutanen da suka karbi katikan zabe.

A yankin kudu maso yamman an karba katikan zabe miliyan 18.2, sai yankin kudu maso yamma dake biye da ita da miliyan 12.8.

Arewa ta tsarina na da miliyan 11.5 , sai yankin kudu maso kudu da ke da miliyan 11.1.

Yankuna masu karancin katikan zaben na dindindin kuwa sune kudu maso gaba da arewa maso gabas.

Duk da mun samu rahoton gobara a was ofisoshin hukumar na wasu jihohin kudu maso gabas, haka ba zai sa muce shine musabbabin karancin katikan zabe a yankin ba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel