Hare-haren Katsina: Mutanen yankin sun fara komawa Batsari a matsayin masu gudun hijira

Hare-haren Katsina: Mutanen yankin sun fara komawa Batsari a matsayin masu gudun hijira

- Mutanen da garin gashi ya rusta dasu a katsina sun koma Batsari

- Sun gudu ne saboda halin firgici da suka tsinci kan su a ciki

- Yan sanda sunyi kira garesu da su kwantar da hankulansu

Hare-haren Katsina: Mutanen yankin sun fara komawa Batsari a matsayin masu gudun hijira
Hare-haren Katsina: Mutanen yankin sun fara komawa Batsari a matsayin masu gudun hijira
Asali: Depositphotos

Sama da mutane 1,300 ne wadanda harin fashi da makami ya rutsa da su a garin katsina suka yi gudun hijra suka bar garin a satin da ya gabata. Su dai wadannan yan gudun hijira mazauna katsina sun gudu ne inda suka koma Batsari domin neman mafaka.

Yawancin su dai mazauna garuruwan sabon garin Dan Buran, Garin Labo, Kwandatso, Garin Yara, Shigi, Garin Dodo, Dan Gudun-wada da sauransu. Su dai yan fashin sun kai harin ne a kauyen Kasai in da har suka hallaka wani kaftin din soja tare da kashe karin mutane guda uku.

GA WANNAN: Hukumar Kwastam na kan bincike kan harbi da bindiga, bayan sun halbe wani murus

Me magana da yawun bakin yan sandan katsina Gambo Isah yace zasu yi iya bakin kokarinsu domin ganin sun magance wannan matsalar da take nema ta addabi mutane a garin.

Sannan ya bukaci jamaa da su kwantar da hankulan su su kuma bawa jami'an tsaro hadin kai don ganin an gama da matsalar fashin gabadaya domin kuwa sun shirya tsaf kuma sun gama duk tsare tsaren su.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel