'Yan ta'adda sun hallaka babban soja da Mutane 6 a jihar Katsina

'Yan ta'adda sun hallaka babban soja da Mutane 6 a jihar Katsina

Rahotanni kamar yadda shafin jaridar Vanguard ta ruwaito sun bayyana cewa, wani babban jami'in tsaro tare da fararen hula shida sun rasa rayukan su a sanadiyar aukuwar wani mummunan hari cikin kauyen Kasai da ke karamar hukumar Batsari.

Wani babban jami'in rundunar dakarun sojin Najeriya tare da wasu Mutane shida sun rasa rayukan su a sakamakon aukuwar wani mummunan hari na 'yan bindiga cikin kauyen Kasai da ke karkashin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

'Yan ta'adda sun hallaka babban soja da Mutane 6 a jihar Katsina

'Yan ta'adda sun hallaka babban soja da Mutane 6 a jihar Katsina
Source: Twitter

Lamarin kamar yadda manema labarai suka ruwaito ya auku ne a karshen makon da ya gabata. 'Yan bindiga ba bu zato ba bu tsammani sun kai hari cikin kauyen tare da yiwa babban sojan kwanton bauna kuma daga bisani suka hallaka wasu Mutane shida nan take.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, 'yan bindigar kimanin 100 sun yin tururuwa wajen zartar da wannan mummunan hari a kauyen Kasai bayan haurowa daga Dajin Rugu da ke kan iyaka guda da garin Batsari.

Gwamnan jihar Kastina, Aminu Bello Masari tare da tawagar sa da ta hadar da kwamishinan 'yan sandan jihar, Sule Buba da kuma Birgediya Janar Luqman, sun yi tattaki wajen kai ziyara zuwa kauyen Kasai domin jajantawa al'umma.

KARANTA KUMA: Makiyaya sun hallaka Mutane 16 a jihar Benuwe

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, bayan zatar da ta'addanci a jihar ta Katsina da ta kasance mahaifa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, maharan sun kuma yi awon gaba da dukiyar al'umma da ta hadar da Babura gami da dabbobin su na kiwo.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel