NAF ta yi bajakolin ‘yan bindigar da ta kama a Kaduna, hotuna

NAF ta yi bajakolin ‘yan bindigar da ta kama a Kaduna, hotuna

Rundunar sojin sama (NAF) ta 453 da ke jihar Kauna ta bayyyana cewar ta kama wasu ‘yan bindiga 10 da ake zargi da aikata laifukan ta’addanci tare da kwace shanu 57 daga hannun su.

A jawabin da ya gabatar ga manema labarai a Kaduna, kwamandan bayar da horo ga rundunar NAF da ke Karina, Air Commodore Idi Sani, ya ce; “a ranar 16 ga watan Fabrairu, 2019, dakarun rundunar sojin sama sun yi nasarar kama wasu ‘yan daba da ‘yan bindiga 7 a jihar Kaduna.

‘Yan bindigar da aka kama su ne: Abdullahi Adamu, Halilu Rilwan, Lawal Hassan, Idris Yusuf, Kabir Muhammad, Badamasi Alhassan da Idris Abubakar. An kama su dauke da muggan makamai a kusa da sansanin alhazai da ke Mando.

“’Yan bindigar 7 sun yi ikirarin cewar su ‘yan kungiyar bijilanti ne da ke kan hanyar su ta zuwa kauyen Buruku a karamar hukumar Chikkun da ke nan jihar Kaduna.

NAF ta yi bajakolin ‘yan bindigar da ta kama a Kaduna, hotuna
NAF ta yi bajakolin makamai da ‘yan bindigar da ta kama a Kaduna
Asali: Twitter

NAF ta yi bajakolin ‘yan bindigar da ta kama a Kaduna, hotuna
NAF ta yi bajakolin ‘yan bindigar da ta kama a Kaduna
Asali: Twitter

NAF ta yi bajakolin ‘yan bindigar da ta kama a Kaduna, hotuna
NAF ta yi bajakolin ‘yan bindigar da ta kama a Kaduna
Asali: Twitter

“A dai ranar 16 ga watan na Fabrairu, dakarun NAF sun yi nasarar cafke Abdulrauf Yusuf wanda aka fi sani da ‘Gorilla Fighter’ tare da wani abokin sa mai suna Muhammad Bello. An kama su ne a daidai kwanar ofishin NECO da ke Mando a cikin wata jar mota kirar Golf 3 mai lambar mallaka kamar haka: EG181ABS Abuja.

DUBA WANNAN: CUPP ta bukaci DSS ta kama Lawal Daura saboda yin sojan gona

Kwamanda Sani ya kara da cewa, “a ranar 15 ga watan Fabrairu, mun kama Shehu Yahaya a kasuwar Amana.

“Mun yi nasarar samun wata mota kirar Golf 3 mai lambar mallaka kamar haka: EG181ABS Abuja, wata motar marar lamba, bindigu 8, adda 5, wuka 1 da wasu manyan wukake 10 da kuma shanu 57.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel