Bai kamata sojoji suyi aikin tsaro a zabe ba, na 'yansanda ne aikin - Babban Provost na hukumar

Bai kamata sojoji suyi aikin tsaro a zabe ba, na 'yansanda ne aikin - Babban Provost na hukumar

- Bai kamata a sanya sojiji cikin sha'anin zabe ba

- Idan har ana neman zaman lafiya a Najeriya a zaben shekara ta 2019 ya zama dole INEC da duk wata hukuma ta gwamnati wanda ya hada da hukomomin tsaro ya zama dole su bi tsari daya

- A wannan duniyar ta yanzu idan har ana bukatar tsaro ya zama tilas a samu hadin kan kungiyoyi da al'umma

Bai kamata sojoji suyi aikin tsaro a zabe ba, na 'yansanda ne aikin - Babban Provost na hukumar
Bai kamata sojoji suyi aikin tsaro a zabe ba, na 'yansanda ne aikin - Babban Provost na hukumar
Asali: Facebook

A jiya ne tsohon provost na hukumar sojojin Najeriya Brigadier General Idada Ikponwen (retd) ya bayyana cewa wani sabon abune wanda ba'a saba dashi ba yin amfani da sojoji a harkar zabe dama sauran abubuwa wanda bai shafi soja ba.

Ya bayyana cewa bada gudummawa a harkar zabe aikin yan sanda ne.

Idan har ana bukatar tsaro a sha'anin zaben shekara ta 2019 ya zama dole hukumar zabe ta kasa (INEC) da ragowar hukumomin tsaron da suka shiga cikin tsa'anin subi hanya daya.

GA WANNAN: Gargadin karshe da APC ta yiwa Turawan Yamma: Kuji da matsalolinku na tattalin arziki

A duniyar yanzu idan har ana bukatar tsaro ya zama tilas a samu hadin kan kungiyoyi da al'umma wanda sune ya kamata a bawa muhimmanci sosai.

Daga karshe ya kara da cewa "jami'an soja basu da hurumin shiga tsare tsaren zabe idan har ba umarni ne daga shugaban kasa na majalisar tarayya ba".

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel