Satar akwati: Buhari be bayar da umarnin a kashe kowa ba - Tinubu

Satar akwati: Buhari be bayar da umarnin a kashe kowa ba - Tinubu

Babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yayi bayani da kuma Karin haske gae da umurnin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba hukumomin tsaro a ranar Litinin, 18 ga watan Fabrairu.

Tinubu wanda yayi magana bayan taron shugabannin APC a Abuja, inda Shugaban kasa ya bayar da umurnin cewa ayi maganin masu satar akwatin zabe yayinda kasar ke shirye-shiryen zabenta da aka dage.

Satar akwati: Buhari be bayar da umarnin a kashe kowa ba - Tinubu
Satar akwati: Buhari be bayar da umarnin a kashe kowa ba - Tinubu
Asali: UGC

Tinubu yace: "Ina a ganawar, kawai dai Shugaban kasar ya jadadda gaskiyar lamari ne cewa idan ka fito kwace akwatunan zabe ko ka tayar da rikici, kana barazana ne ga rayuwarka. Duk abunda ya same ka, babu Shugaban kasar da zai bayar da umurnin harbe alúmman kasarsa, A’a! A’a, yayi, raunin zukata yayi yawa yan kwanakin nan. Ana iya yiwa kowa kuskuren fahimta harda ni.

KU KARANTA KUMA: Ina iya rantsewa da Qur’ani cewa INEC ta sanar da PDP batun dage zabe - Oshiomhole

"Umurnin harbi ba kalamunsa bane, mutum ne mai bin doka sannan ya san abunda doka ta kunsa da kuma girman rayuwar mutanen kasa, ya san da cewa yana akan wannan mukamin na kare rayuka."

A baya dai mun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi masu shirin tayar da tarzoma a ranan zabe da cewa su nisanci akwatunan zabe ranan Asabar, 23 ga watan Febrairu, 2019.

A wata ganawar gaggawa da jigogin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sukayi ranan Litinin a birnin tarayya Abuja, shugaban kasa ya ce duk wanda ya tayar da rikici musamman ta hanyar daukan akwatin zabe, to abkin ransa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel