Mohammed Salman na so yayi cinikin Manchester a kan kudi Biliyan $3.8

Mohammed Salman na so yayi cinikin Manchester a kan kudi Biliyan $3.8

- Mohammadu Dan Salman yana so ya saye Kungiyar Manchester United

- Yarima Salman yana neman yadda za a saida masa kulob din ne tun bara

- Matashin Mai shekaru 33 da haihuwa zai yi kungiyar tayin Dala Biliyan 3.8

Mohammed Salman na so yayi cinikin Manchester a kan kudi Biliyan $3.8

Mohammed Salman yana so a saida masa Kulob din Man Utd
Source: Getty Images

Mun ji labari cewa Mohammad Dan Sarki Salmanu na kasar Saudiyya yana so a saida masa kungiyar nan ta Manchester United wanda tayi fice a Duniya. Salmanu zai jarraba sa’ar sa wajen ganin ya saye babban kulob din.

Kamar yadda mu ka samu labari, Mohammad Dan Sarki Salmanu zai mikawa Gidan Glazers kudi wuri na gugar wuri har Dala biliyan 3.8 domin ganin ya saye kungiyar kwallon kafan na kasar Ingila mai dinbin tarihi a Duniya.

KU KARANTA: Ina nan a kan baka ta na sayan Kungiyar Arsenal - inji Dangote

Gidan Glazer sun saye kulob dinnen shekaru fiye da 10 da su ka wuce a kan kudi Dala miliyan £790. Idan har Glazer su ka amince da wannan tayi na Yariman na Saudiyya, za su samu ribar da ta haura ta Dala biliyan 2.2 nan take.

Jaridar nan ta Sun ta kasar Ingila ta rahoto cewa Yarima Salman yana so Manchester United ta shigo hannun sa ne kamar yadda Gidan Sheikh Mansour su ka karbe kungiyar Man City masu makwabtaka da Manchester United.

Saurayin mai shekaru kusan 33 a Duniya zai so ya jira zuwa karshen kakar bana ya tabbatar cewa kungiyar za ta kara a gasar Zakarun Nahiyar Turai kafin ya sa kudin sa a kulob din. Yanzu dai Man Utd tana kan mataki na 4 ne a tebur.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel