Sanatan APC ne ya yi kwangilar kayan aikin zabe – Shugaban INEC
A jiya, Asabar, ne shugaban hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya amsa cewar sanatan jam’iyyar APC mai wakilta jihar Neja ta gabas, Sanata Mohammed Musa, na daga cikin ‘yan kwangilar hukumar.
Shugaban na INEC ya bayyana haka ne yayin wani taro na ma su ruwa da tsaki da aka yi a cibiyar taro ta kasa da kasa da ke Abuja.
Tun a kwanakin baya ne dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewar INEC ta bayar da kwangilar sayen injinan buga katinan zabe (PVC) ga kamfanin ‘Activate Technologies Limited’ mallakar sanatan jam’iyyar APC, Mohammed Sani Musa.
A cikin jawabin, Atiku ya nuna shakku a kan dalilin hukumar INEC na bawa kamfanin Sanata Musa kwangilar saye tare da dasa na’urorin a hedikwatar hukumar.
Atiku ya kara da cewa, “duk da kasancewar Sanata Musa na da hakkin yin kasuwanci da kuma rike mukami a gwamnati, amma bai dace INEC ta bashi kwangilar saye da kafa na’urori ma su muhimmanci d bukatar sirri ba saboda kasancewar sad an jam’iyyar APC da za a fafata da ita a zabe ba.”
Da ya ke amsa tambaya daga Osita Chidok, wakilin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, shugaban na INEC ya bayyana cewar ya na da masaniyar cewar dan kwangilar na takarar kujerar sanata a jam’iyyar APC.
DUBA WANNAN: ‘Yan bindiga sun kai hari gidan dan takarar majalisar tarayya na APC
Sai dai ya bawa ‘yan Najeriya tabbacin cewar hakan ko kadan ba zai shafi kima da sahihancin zaben da INEC za ta gudanar ba.
A cewar sa, “ina sane cewar mai kamfanin dan takarar kujerar sanata ne a jam’iyyar APC. Kamfanin tun shekarar 2011 ya ke yi wa INEC kwangila. Ina mai tabbbatar ma ku da cewar hakan ba zai shafi kima ko sahihancin zaben da za mu gudanar ba."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng