An gano sakamakon jarrabawar karshe da yarinyar nan mai kwazo Leah tayi, kafin bautar Boko Haram

An gano sakamakon jarrabawar karshe da yarinyar nan mai kwazo Leah tayi, kafin bautar Boko Haram

- Sakamakom jarabawar Leah Sharibu na kammala karamar sakandare ya bayyana

- Sakamako ne mai kyau domin A tara da B uku

- A karatowar zaben nan yakamata mu tuna da Sharibu

Sakamakon Jarrabawar Leah
Sakamakon Jarrabawar Leah
Asali: UGC

Jarabawar kammala aji uku na sakandaren Leah Sharibu, yarinyar da labarinta ya bazu. Tana cikin garin da ke da karancin ilimi. Amma sakamakon jarabawarta ya bayyana da A tara da B uku, Leah na nan tana bauta a dajin Al-Barnawi.

Ko albarkacin zabe bai sa gwamnati ta waiwayeta ba. Ba a ko ambaton sunan ta yayin kamfen din zabe.

GA WANNAN: Gani Adams na OPC a kasar Yarabawa, yace a zabi mai tsoron Allah a zabukan 2019

Da farko dai wadanda suka sace ta sun karba makudan kudade inda suka sako sauran yam matan amma suka ki sakin Sharibu sakamakon rashin barin addininta da tayi.

A yanzu da zaben shugabancin kasa ya koma asabar mai zuwa, yakamata mu tuna da ita. Duk da ba dole mu iya taimakon ta ba, amma lokacine da zamu iya tunawa da ita.

Sharibu tasan tana zukatan mu, baza mu taba mantawa da ita ba.

Boko Haram dai ta bautar da Leah Sharibu a yankin Sahel inda ISIL take kokarin kafa sansani shekara guda kenan, kawai don ta zabi addinin da ba irin wanda suke so ba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel