Bincike ya tabbatar akwai isashshen sinadarin iskar gas a Gombe da Bauchi – shugaban NNPC

Bincike ya tabbatar akwai isashshen sinadarin iskar gas a Gombe da Bauchi – shugaban NNPC

Shugaban hukumar kula da man fetir na Najeriya, NNPC, Dakta Maikanti Baru ya yi karin haske kan binciken hakar danyen mai da suka kaddamar a tafkin Kolmani II dake kusa da kauyen Barambu cikin karamar hukumar Alkalerin jahar Bauchi.

Baru yace makasudin kaddamar da binciken hakar man shine domin akwai bukatar kara yawan adadin man fetir da iskar a Najeriya ta hanyar binciko duk ake ganin akwai sinadaran tare da hakosu.

KU KARANTA: Wani Sanata daga cikin Sanatocin Najeriya ya tsallake rijiya da baya a hadarin mota

Bincike ya tabbatar akwai isashshen sinadarin iskar gas a Gombe da Bauchi – shugaban NNPC
Buhari da shugaban NNPC
Asali: UGC

Legit.ng ta ruwaito Baru na tabbatar da cewa akwai sauran wurare guda shida a tafkin Kolmani da suke sa ran samun mamakon danyen mai jibge a wuraren, amma daya bayan daya zasu dinga binsu, inda ya kara da cewa da wannan sun cika umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya basu.

Sai dai shugaban na NNPC ya bayyana cewa suna fuskantar babbar kalubale wajen cigaba da aikin hakar man fetir a tafkin Chadi dake yankin Arewa maso gabashin kasar nan, sakamakon matsalar tsaro data dabaibaye yankin.

Bugu da kari yace wannan ne dalilin da yasa suka rabu da tafkin Chadi suka dawo kolmani, wanda yace dama tun a shekarar 1999 kamfanin SNEPCO ta fara aikin hakar man, inda ta hako rijiyan mai guda daya, su kuma a yanzu suka hako rijiya na biyu.

“A lokacin da suka gano rijiyan farko, sai suka tarar da iskar gas din dake jibge a kasan bashi da yawa, a cewarsu bai kai abinda za’a iya sayarwa a kasuwannin duniya ba, don haka suka tashi, mu kuma da muka zo sai muka sake gudanar da bincike, wanda ya nuna mana akwai isashshsen iskar gas, sai dai SNEPCO basu haka kasa sosai bane.” Inji shi.

Maikanti yace idan har suka samu nasarar hako iskar gas din da suke tunanin akwai tafki Kolmani, hakan zai amfani Najeriya sosai, musamman yankin Arewa saboda za’a kafa kamfanonin wutar lantarki, kamfanonin hada takin gona, kamfanonin hada sinadarna kemikal.

Daga karshe yace zuwa yanzu jama’an yankin Kolmani sun fara cin gajiyar aikin da NNPC ke yi a wajen, inda yace sun gina rijiyoyin burtatsi guda 27 saboda matsalar karancin ruwa a yankin, suna gina kananan asibitoci kuma, muna gyara makarantunsu, kuma muna da burin zamanantar da kauyukan dake yankin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel