Manyan Malaman addinin Musulunci sun yi kaca-kaca da Kwankwaso

Manyan Malaman addinin Musulunci sun yi kaca-kaca da Kwankwaso

- Jawabin da Kwankwaso yayi a kan Malaman da ke shiga siyasa bai yi wa jama’a dadi ba

- Wasu manyan Malamai da ake ji da su a kasar nan sun fito sun yi kaca-kaca da Sanatan

Manyan Malaman addinin Musulunci sun yi kaca-kaca da Kwankwaso

Malamai sun ji haushin maganar Kwankwaso a kan gemu
Source: Twitter

Mun samu labari cewa wani jawabi da Sanatan Kano ta tsakiya watau Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso yayi a kan barin gemu da kuma digile wando ya fusata wasu manyan Malaman Ahlul Sunnah musamman na Arewa.

A cikin ‘yan kwanakin nan ne Kwankwaso ya caccaki wasu malaman addini da yace su ke tsoma baki cikin harkar siyasa. Tsohon gwamnan ya kira wadannan Malamai da Magada Daloli wadanda su ka saba sabawa Allah madaukaki.

KU KARANTA: Kwankwaso ya yabawa Marigayi Sheikh Jafar Adam a wajen kamfe

Sai dai manyan Malaman Ahlul-Sunnah irin su Sheikh Abdullahi Gadon-Kaya sun yi Allah-wadai da irin wannan magana da ta fito daga bakin Sanatan. Shehin Malamin yace babu wanda ya isa ya taba Malamai da ke da mutunci.

Shi ma Sheikh Abubakar Lawal wanda aka fi sani da Triumph yayi tir da kalaman tsohon gwamnan lokacin da yake karatu a Kano. Haka kuma Sheikh Abdulwahab Abdallah ya gargadi ‘yan siyasa su guji taba Sunnar Manzon Allah.

A cikin ‘yan kwanakin nan ma, babban Malamin kungiyar Izala, Sheikh Abubakar Giro Arugungu ya tsinewa babban ‘dan siyasar inda yayi masa kaca-kaca na yin fito-na-fito da sunnar Ma’aikin Allah.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel