Har a kotu, Atiku Abubakar ya kasa yi wa jama'a bayani kan zarginsana suwaye daga dangin Buhari masu 9-mobile

Har a kotu, Atiku Abubakar ya kasa yi wa jama'a bayani kan zarginsana suwaye daga dangin Buhari masu 9-mobile

- An shiga kotu a rana ta farko kan karar

- Bangaren Baba Buhari sun kai qara ne kan yadda Atikku ya ci masu

- Atiku yace iyalan Buhari ke da Keystone bank da 9-mobile

Har yanzu Atiku Abubakar ya kasa yi wa jama'a bayani kan zarginsana suwaye daga dangin Buhari masu 9-mobile

Har yanzu Atiku Abubakar ya kasa yi wa jama'a bayani kan zarginsana suwaye daga dangin Buhari masu 9-mobile
Source: Facebook

Alkaliya Binta Muhammed ta saurari karar da kungiyar masu goyon bayan Buhari suka shigar, BSO, kan yadda wai Atiku ya yanka wa iyalin shugaba Muhammadu Buhari karya kan wai da shi da iyalansa suka saye banki na Keystone da 9-mobile.

Har yanzu Atiku Abubakar ya kasa yi wa jama'a bayani kan zarginsana suwaye daga dangin Buhari masu 9-mobile

Har yanzu Atiku Abubakar ya kasa yi wa jama'a bayani kan zarginsana suwaye daga dangin Buhari masu 9-mobile
Source: UGC

Sai dai bangaren Atikun sun kasa kare kansu kan batun, lamari da ya ja cece-kuce a kasar nan lokacin da Atikun yayi zargi.

Kafin a dage sauraron karar, lauyan masu kara, Barr Abdulrazaq Ahmed, ya sanar da kotun cewa an bashi takardar kariya, da bukatar Naira biliyan 200 da kuma bukatar watsi da karar saboda kungiyar ba mai rijista bace.

Ahmed yace, "An ba kungiyar damar maida martani ga masu kariyar akan ikirarin su a cikin kwanaki 7." Sakamakon kin lauya mai kare wanda ake kara na maida martani yasa mai shari'a Mohammed ta dage sauraron karar.

Amma kuma babu wata takardar shaida da lauyan da ke kare Atiku ya mika don tabbatar da ikirarin da yayi.

A sakin layi 18 na takardar da lauyan Atiku ta mika, tayi korafi ne kadai akan cewa ba a mika karar ta yanda ya dace ba, tare da kara jaddada cewa babu ta inda kalaman suka bata sunan Buhari.

Ana dai yawan zargin wasu sun kankane a gwamnatin Buhari suna neman kudi, shi kuma an barshi yana yaki da rashawa kan 'yan PDP. Zargi da APC ta sha karyatawa.

An dai dage karar zuwa 7 ga watan Maris bayan manyan zabuka don ci gaba da sauraren bahasin bangaren masu kare kansu.

GA WANNAN: Kaje gida ka huta! Baka bukatar aiki bayan ritaya - Junaid ga dattijo Buhari

A nasu bangaren, lauyoyin Atiku, sunce ai kungiyar ma ta BSO batta da rajissta don haka batta da hurrumin shigar da qara da sunan wasu.

Ana gab dai a shiga zabe wanda zai iya maida Atikun shugaba, wanda zai kashe karas gaba daya.

A yanzu dai za'a iya cewa zargin na Atiku bashi da makama babu kumma hujja.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel