Yadda ake sace namun dajin Najeriya a sayar da makudan daloli a kasashen ketare

Yadda ake sace namun dajin Najeriya a sayar da makudan daloli a kasashen ketare

- Hukumar Kwastam ta Najeriya tace ta kama sama da dalar Amurka miliyan kusan $900m na safarar dabbobin daji

- Pangolin dai wata dabba ce wadda ake samu a kasashen Asiya da Afirka

- Ana safarar ta a matsayin abinci, magani da kuma kayan ado

Yadda ake sace namun dajin Najeriya a sayar da makudan daloli a kasashen ketare

Yadda ake sace namun dajin Najeriya a sayar da makudan daloli a kasashen ketare
Source: UGC

An dade dai ana sace dabbobi daga kasashen Airka a kai su kasashen Turai da Asiya, ko don kudi ko don kawa, tun zamanin mulkin mallaka.

Yanzu dai da yawa daga dabbobin da ake tsoron zasu bace daga doron kasa an hana a kama su ko don ci ko don magungunan surkulle, wadanda 'yan China ke tsubbu dasu, da tsammanin wai zasu yi aiki.

Hukumar Kwastam ta Najeriya, ta bayyana yadda ta kama irin wadannan dabbobi musamman kunkurun kurmi, watau Pangolin, wanda aka yi niyyar kaiwa kasashen waje, har na kudi $900m a kasuwar karkashin kasa.

GA WANNAN: Gwamnatin Tarayya ta dakatar da duk wani matakin shari'ah da take dauka kan Onnoghen - NBA

Hukumar ta bayyana hakan ta bakin mataimakin comptroller Mutalib Sule a yayin da suke gudanar da wani taro da akayiwa lakabi da 2019 World Pangolin day a ranar Laraba a jihar Legas.

Nigerian Conservation Foundation, kungiya mai kula da tattala namun daji dake Lekki jihar Legas tare da hadin gwiwar Pangolin Conversion Guild of Nigeria ne suka hada taron.

Kamfanin dillancin labarai na NAN, ya rawaito mana cewa Pangolin dabba ce wadda take da kaho ana samun ta a nahiyar Africa da Asia.

Mutalib Sule ya kara da cewa "A fadin duniya gaba daya wannan kame na Pangolin da suka yi shine wanda yafi kowanne".

Kasar Japan itace ta biyu a bangaren kwacen inda ta kama 7.100kg wanda yayi daidai da dalar amurka 450,000.

Ita kuma Najeriya ta kama kama wanda adadin kudin ta zaikai dalar amurka $900,000,000.

Ana kama dabbar Pangolin ne wajen amfani da ita a matsayin abinci, magani da kuma kayan ado inda akafi safarar ta zuwa China, Vietnam da kuma ragowar wasu kasashen dake lardin Asia, inda chamfi kan irin wadannan dabbobi yayi katutu.

Ana siyar da giram daya akan dalar Amurka $3,000.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel