Kada ku jefa jahar Kano cikin fitina – Sarki Sunusu II ga yan siyasan Kano

Kada ku jefa jahar Kano cikin fitina – Sarki Sunusu II ga yan siyasan Kano

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya yi muhimmin gargadi da jagororin siyasar Kano da ma yaransu da kada su kuskura su jefa jahar Kano cikin fitintinun siyasa kawai saboda neman wasu bukatunsu na siyasa.

Legit.ng ta ruwaito Sarkin ya yi wannan kira ne a ranar Talata, 12 ga watan Feburairu, yayin da yake ganawa da manema labaru a fadarsa dake cikin birnin Kano, inda ya bayyana matsayin masarautar Kano game da farfadowar ayyukan yan barandan siyasa a garin.

KU KARANTA: Akwai matsala: Akwai marasa aikin yi guda 4,000,000 a tsakanin jahar Kano da Jigawa

Kada ku jefa jahar Kano cikin fitina – Sarki Sunusu II ga yan siyasan Kano
Sarki
Asali: UGC

Sarkin yace ya zama dole ya yi wannan kira ga jagoroin yan siyasa, duba da yadda suke tunzura matasa suna cin mutuncin mutanen da basu ji ba basu gani ba, inda suke bin wasu har cikin gidajensu gaban iyalansu.

“Mun yanke shawarar ganawa da manema labaru ne bisan rahotannin da muka samu dake nuna akwai babbar barazana ga rayuwar jama’an Kano da dukiyoyinsu. Muna kira da a zauna lafiya tsakanin yan siyasa da jama’an gari.

“Siyasa fa ba yaki bane, idan har kana da katin zabe, sai ka zabi duk wanda ya kwanta a maka rai ya zama shugabanka.” Inji Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II.

Sarkin ya yi kira ga yan siyasa dasu kiyayi jaye jayen mutanen da basu sansu ba, domin kada su aikata munanan ayyuka da sunansu, don haka yayi kira ga hukumomin tsaro dasu tashi tsaye wajen gudanar da aikinsu tare da kama duk wasu miyagun mutane.

Bugu da kari Sarkin ya yi kira ga hakiman Kano 44 dasu tabbata sun bada goyon baya da hadin kai ga hukumomin tsaron ta hanyar mika duk wasu wadanda suka aikata laifi ga hukumar Yansanda ba tare da bata lokaci ba.

Daga karshe Sarkin yayi addu’ar Allah Yasa a gudanar da zaben 2019 cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare da yin kira ga jama’a dasu kasance masu biyayya ga doka da oda a jahar Kano da ma kasar gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel