Farmakin gidan Abdullahi Abbas: Rundunar ‘yan sanda ta kama ‘yan daba 28 a Kano

Farmakin gidan Abdullahi Abbas: Rundunar ‘yan sanda ta kama ‘yan daba 28 a Kano

Sabon kwamishinan rundunar ‘yan sanda a jihar Kano, Mista Moohammed Wakili, y ace jami’an rundunar ‘yan sanda sun kama wasu batagari 28 bisa alakar da su ke da ita da harin da aka kai gidan shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano, Abdullahi Abbas, yayin taron yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP da aka yi jiya, Lahadi, a Kano.

A jiya ne rahotanni su ka bayyana cewar wasu ‘yan daba da ake zargin na yiwa jam’iyyar PDP aiki sun kai farmaki gidan shugaban jam’iyyar tare da raunata dan sa da wasu mutane biyu.

Da ya ke jawabi ga manema labarai a yau, Litinin, a hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta Kano da ke unguwar Bompai, Wakili ya ce an fara gudanar da bincike a kan lamarin tare da bayyana cewar rundunar ‘yan sanda za ta dauki mataki a kan duk wanda ke da hannu a kan afkuwar lamarin, duk girma ko matsayin sa.

Wakili ya bayyana cewar a shirye ya ke domin ganin cewar an samu zaman lafiya a jihar Kano kafin da kuma bayan kamala zabe. Kazalika ya yi kira ga ‘yan siyasa da su kasance ma su girmama doka tare da bayar da tabbacin cewar rundunar ‘yan sanda za ta kasance mai adalci ga kowa da kowa.

Farmakin gidan Abdullahi Abbas: Rundunar ‘yan sanda ta kama ‘yan daba 28 a Kano
Taron Atiku a Kano
Asali: Facebook

Ba zamu bar wasu ‘yan tsiraru daga cikin mu su ke aikata duk abinda ran su ke so, tamkar babu doka, ba. Ba zamu bari su mayar da Kano tamkar turken tumaki ba. Ba zamu sake bari abinda ya faru ranar Lahadi, 10 ga watan Fabarairu, ya sake faruwa ba a jihar Kano.

DUBA WANNAN: Zalunci: An kama wasu ma’aikatan INEC da laifin karbar kudin ma su katin zabe

“Dokar Najeriya ta haramta dauka tare da amfani da muggan makamai yayin taron siyasa ko yakin neman zabe ba.

“Su na amfani da ‘ya’yan talakawa wajen tayar da husuma, yayin da ‘ya’yan sun a can kasashen ketare sun a karatu. An saka hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya kuma ina kira ga dukkan ‘yan takara da su girmama wannan yarjejeniya,” a kalaman kwamishina Wakili.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel