Za mu yi maganin ‘Yan ta’addan Najeriya – Janar Tukur Buratai

Za mu yi maganin ‘Yan ta’addan Najeriya – Janar Tukur Buratai

- Janar Tukur Yusuf Buratai yace za su rusa shirin Boko Haram da ISWA

- Ana tunanin cewa ‘Yan ta’addan ISWA su na karawa Boko Haram karfi

- Shugaban sojojin kasar yace Dakarun sa za su kauda duk ‘Yan ta’addan

Za mu yi maganin ‘Yan ta’addan Najeriya – Janar Tukur Buratai

Tukur Buratai yace za su hana ISWA da Boko Haram sakat
Source: Depositphotos

Mun ji labari cewa shugaban hafsun sojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai, ya bayyana cewa zai yi kokari wajen ganin ya rusa hadin-gwiwar da aka samu tsakanin ‘Yan ta’addan Boko Haram da kuma Takwaran su na ISWA.

Laftana Janar Tukur Buratai yayi wannan jawabi ne dazu a Abuja wajen wani taron kwana 2 da aka shiryawa manyan sojojin Najeriya. Janar Buratai ya kuma bayyana cewa su na samun galaba a kan ‘yan ta’addan Boko Haram.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya furta cewa zaben 2019 na fuskantar cikas

Shugaban sojojin kasar yake cewa Dakarun sa na cigaba da lallasa ‘yan ta’addan na Boko Haram da su ke Arewa maso gabashin kasar a yunkurin da sojoji ke yi na ganin an rusa shirin da aka kulla tsakanin Boko Haram da ISWA.

Manjo Janar Aliyu Nani wanda ya wakilci Janar Tukur Buratai a wajen taron yace rundunar sojin Najeriya su na kuma kara shiga cikin Arewa ta gabas domin ganin an daina jin duriyar ‘yan Boko Haram da su ka addabi jama’a.

Babban sojan na Najeriya dai ya kuma nemi jami’an kasar su guji shiga cikin harkar siyasa ko kuma nuna fifikon su a zaben da za ayi kwanan nan. An dai shirya taron ne domin kara wayar da kan jami’an sojojin na Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel