Sojojin Najeriya sun kashe mutane 2 yayin da rikici ya barke tsakaninsu da jama’an gari

Sojojin Najeriya sun kashe mutane 2 yayin da rikici ya barke tsakaninsu da jama’an gari

Akalla mutane biyu ne suka rigamu gidan gaskiya biyo bayan wani kazamin rikici daya barke tsakanin jama’an gari da wata tawagar Sojojin Najeriya a unguwar Ejemekwuru dake cikin karamar hukumar Oguta ta jahar Imo.

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito ana zargin mutanen da suka afka ma Sojojin da cewa gungun matasan kungiyar asiri ne, wannan lamari ya faru ne a ranar Asabar, 9 ga watan Feburairu a yayin da gwamnan jahar Imo, Anayo Rochas Okorocha ke gudanar da gangamin yakin nemna zabensa.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan majalisa a jahar Sakkwato

Shi dai Gwamna Rochas zai kammala zangon mulkinsa guda biyu daya faro daga shekarar 2011, kuma a yanzu haka shine dan takarar Sanatan jam’iyyar APC a jahar na mazabar Imo ta yamma a zaben da zai gudana a ranar 16 ga wata.

A yayin da ake tsaka da gudanar da gangamin yakin neman zaben, inda gwamnan ke farautar kuri’un jama’a ma kansa da dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar APC, Muhammadu Buhari ne sai wasu matasa Tochi da Ndukwe suka fara dambe da Sojojin dake bayar da tsaro a wurin taron.

Nan fa rikici ya barke, inda nan take Sojojin suka bindige matasan biyu, kamar yadda majiyarmu ta bayyana. Sai dai kwamishinan Yansandan jahar, Dasuki Galadanchi ya tabbatar, amma yace matashi daya Sojojin suka harba, kuma sun yi hakan yayin da suke gudanar da sintiri a yankin.

Haka zalika kwamishina Dasuki yace Yansanda sun shawo kan lamarin, kuma tuni hankula suka kwanta a garin, amma yace sun samu nasarar kama mutane hudu dake da hannu cikin tayar da zauni tsaye a yankin.

Dasuki ya cigaba da tabbatar da aukuwar lamarin inda yace gaba daya rikicin ya samo asali ne daga yan kungiyar asiri, kuma harbe harben da Sojoji suka yi sunyi shi ne a wajen farfajitar yakin neman zaben.

Sai dai jam’iyyar adawa a jahar Imo, jam’iyyar PDP ta bakin kaakakin yakin neman zaben dan takarar gwamnanta, Emeka Ihedioha, Kissinger Ikeokwu a ta danganta wannan kisa ga Gwamna Rochas, sa’annan tayi kira ga rundunar Yansandan jahar da ta kaddamar da bincike.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng