Lauyan Shagari ya kwashe wa 'yan siyasar zamani albarka, ya rage daya tal

Lauyan Shagari ya kwashe wa 'yan siyasar zamani albarka, ya rage daya tal

- Da ace ni ubangiji ne dana turo wuta da tsawa sun kone duk yan siyasar Najeriya, cewar Robert Clarke

- Duk da cewa na manyanta ina jin kaina tamkar matashi

- Najeriya bata taba samun shugaba ba saidai yanzu muna da Buhari

Da ina iyawa kwarankwatsa zan aikowa duk yan siyasar Najeriya - SAN
Da ina iyawa kwarankwatsa zan aikowa duk yan siyasar Najeriya - SAN
Asali: Depositphotos

Tsayin shekaru 50 Robert Clarke ya kasance lauya (SAN) a yayin da yake da shekaru 81 a duniya ya zanta da manema labarai akan wasu abubuwa da suka gabata a rayuwar sa.

A hira da yayi da jaridar Punch, dattijon ya kwashe wa ilahirin 'yan siyasar Najeriya albarka, inda ya kira su mahandama da babakere, yya kuma roki Allah ya tarwatsa muguwar aniyarsu.

GA WANNAN: EFCC tayi ram da Jamila Shu'aibu da abokan damfararta a Abuja

Mr Clarke ya bayyana cewa duk da kasancewar shi dattijo dan shekara 81 a koda yaushe yanajin kansa tamkar wani matashi.

An tambayi Clarke cewa alakar shi da yara ne ya janyo yake jinsa tamkar matashi ko kuwa?

Ya bada amsa da cewa "Abinda yake cutar manyan mu a yanzu shine kadaici, a halin yanzu ni bana tare da wannan saboda kasancewa ta zagaye da kananun yara na."

"Allah ya azurtani da yara Uku, inda babbar take karanta bangaren Shari'a a kasar Ingila".

A cewarsa dai, inda yana da dama ya taba yi wa Shehu Shagari lauya a 1979 lokacin da ya zama shugaban Najeriya, kumma yanzu yana tare da Buhari a kokarinsa na kawo karshen rashawa.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel