Kabilar Fulani sunyi wa Buhari alkawarin kuri'u 11m a makon gobe

Kabilar Fulani sunyi wa Buhari alkawarin kuri'u 11m a makon gobe

- Sunan su Jonde -Jam Fulani Youth Association of Nigeria

- Sunce zasu mara wa Buhari baya ba Atiku ba

- Zaben sauran mako daya ayi shi

Kabilar Fulani sunyi wa Buhari alkawarin kuri'u 11m a makon gobe
Kabilar Fulani sunyi wa Buhari alkawarin kuri'u 11m a makon gobe
Asali: UGC

Wata kungiyar Fulani ta matasa, tayi alkawarin maka wa shugaba Buhari kuri'u har 11m, wadda tace saka wa alheran da yayi ne a lokacin yana aikin soja da ma bayan ya bari.

Jonde -Jam Fulani Youth Association of Nigeria sunan kungiyar, duk da kuma ba'a santa ba, tace zata iya kawo wa shugaban kuri'u har 11m.

Ko a 2015 dai, kuri'u 15 kadai shugaba Buuhari ya samu a duk fadin Najeriyar ma, Hausa da Yarabawa, don haka da kamar wuya su iya hada 11m su kadai.

GA WANNAN: Boko Haram: Yankin mazaba ta yanzu babu matsalar tsaro - Sanata Binta ta Adamawa

Akwai dai kungiyar Miyetti Allah kautal horey, wadda ita ma ta mara wa Buharin baya a kwanan baya, sai dai wani bangare kuna ya koma yace Atiku suke so, lamari da ake gani sakayya ce ta irin gudummawar da yake baiwa bangaren na yankinsu na Adamawa.

Zaben 2019 na nan ya iso gadan-gadan, kuma za'a yi shi ne tsakanin Musulmi da Musulmi, dan arewa da dan arewa, bafillace da bafilace, don haka ma wasu ke ganin bai kamata a dauki zafi ba, tunda duk daga bangare daya suka fito.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel