Karshen yajin aiki: Manyan bukatun Malam jami’a guda 8 da Buhari ya biya musu

Karshen yajin aiki: Manyan bukatun Malam jami’a guda 8 da Buhari ya biya musu

A daren Alhamis, 7 ga watan Feburairu ne kungiyar Malaman jami’o’in Najeriya, ASUU ta janye yajin aikin ‘sai baba ta ji’ data kaddamar tun a ranar 4 ga watan Nuwamba, inda ta dauki alwashin cigaba da yajin aikin har sai gwamnati ta biya mata bukatunta.

Haka kuwa aka yi, kungiyar Malaman ta tubure ta cigaba da daka yajinta ba tare da kakkautawa ko sauraron kiraye kirayen da jama’a mata na ta janye yajin aikin ba, har sai bayan wata tattaunawa da tayi da wakilan gwamnatin tarayya a ranar Laraba.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Kotu ta tsige wani Sanatan APC daga kujerarsa, ta bayyana halastaccen dan takara

Legit.ng ta ruwaito a yayin wannan zaman tattaunawa na karshe ne aka cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya, yarjejeniyar da ta kunshi lalubo hanyoyin biya ma ASUU bukatun da suka sabbaba shigarta yajin aiki, wasu daga cikin alkawurran da gwamnatin shugaba Buhari ta cika ma ASUU sun hada da;

- Biyan naira biliyan 20 a matsayin kudin farfado da jami’o’in Najeriya na shekarar 2018, da kuma alkawarin biyan naira biliyan 25 a watan Afrilu zuwa Mayu, kudin 2019. Daga nan kuma a ta cika aiwatar da yarjejeniyar shekarar 2013

- Biyan wani kaso na alawus din Malamai, tare da tanadin kudin biyan alawus din cikin kasafin kudin 2019

- Biyan cikon albashin Malaman jami’ar noma dake garin Makurdi, zuwa ranar 15 ga watan Feburairu na shekarar 2019

- Karfafa kwamitin tuntunba ta jami’o’in jihohin Najeriya da aka kafa a ranar 28 ga watan Janairu domin ta gudanar da bincike akan matsalolinsu.

- Biyan cikakken hakkokin alawus alawus na malaman jami’ar Illorin, musamman masu yi ma ASUU biyayya zuwa ranar Alhamis 7 ga watan Feburairu.

- Kafa hukumar kula da hakkokin fanshon malaman jami’o’i

- Kaddamar da ziyarar aiki zuwa jami’o’in Najeriya gaba daya daga ranar 11 ga watan Maris.

- Samar da tabbatattun tsare tsare dake nuna rawar da bangarorin biyu zasu taka wajen sake tattauna yarjejeniyar da suka shiga a shekarar 2009, daga ranar 29 ga watan Maris.

Daga karshe shugaban ASUU, Farfesa Biodun Adeyemi ya umarci malaman jami’o’I dasu koma bakin aiki daga ranar Talata, 12 ga watan Feburairu domin cigaba da koyar da dalibai tare da gudanar da sauran ayyukansu kamar yadda suka saba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng