Ruwan wuta: Sojojin sama sun kashe 'yan bindiga da dama a Zamfara

Ruwan wuta: Sojojin sama sun kashe 'yan bindiga da dama a Zamfara

Rundunar Sojin Saman Najeriya NAF ta ce ta tsananta luguden wuta da ta ke yiwa 'yan bindigan jihar Zamfara.

Direktan yada labarai na NAF, Air Commodore Ibikunle Daramola ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis inda ya ce rundunar na Operation Diran Mikiya ta kai wani farmaki a ranar Alhamis.

A cewarsa, an kai farmakin ne bayan anyi amfani da jiragen leken asiri an tabbatar da bayyanan sirrin da aka samu daga bayyanan sirri a da wasu dakarun rundunar suka tattara.

Kakakin NAF din ya ce an gano sansanin da 'yan bindigar ke buya su shirya yadda za su kaiwa al'ummar da ba su san hawa ba balle sauka hari.

Ruwan wuta: Sojojin sama sun kashe 'yan bindiga da dama a Zamfara

Ruwan wuta: Sojojin sama sun kashe 'yan bindiga da dama a Zamfara
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Tsohon janar a rundunar soji ya kwance wa Obasanjo zani a kasuwa

Ya ce, "Anyi luguden wutar na farko ne da asubahin ranar 7 ga watan Fabrairun 2019 a wani wuri cikin dajin Rugu da ke Kudancin Gurbin Baure inda aka gano wasu 'yan bindigan sun taru da motoccin su kusa da mabuyar.

"NAF ta aike da jirgin yaki mai saukan ungulu da Alpha Jet domin yin luguden wuta a kan motoccin da sansanin. An gano 'yan bindigan da dama suna kokarin tserewa daga mabuyar yayin da wasu ke yunkurin tserewa a cikin motoccinsu."

Daramola ya kara da cewa, "Jirgin yakin mai saukan ungulun ya bi motoccin da ke kokarin tserewa inda ya lalata su tare da halaka wadanda ke cikin motocin.

"Alpha jet shima ya yiwa ruwar wuta a kan sansanin inda ya lalata sansanin da harabar ta da 'yan bindigan ke ciki kamar yada aka gano ya kama da wuta.

"Kwararan bayanan sirri ya tabbatar da cewa an kashe 'yan bindigan da dama sakamakon harin."

Kakakin NAF din ya yi bayanin cewa rundunar tana aiki ne da hadin gwiwar dakarun sojin kasa da kuma wasu hukumomin tsaro.

Ya ce za su cigaba da bincike da kai farmaki domin halaka 'yan bindigar da hana su sakat a yankin na Zamfara da kewaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel