Siyasa rigar yanci: Adam Zango ya yi fatali da Buhari, ya koma gidan Atiku a guje

Siyasa rigar yanci: Adam Zango ya yi fatali da Buhari, ya koma gidan Atiku a guje

Shahararren jarumin fina finan Hausa da akafi sani da Kannywood, Adam A Zango na gab da watsa ma shugaban kasa Muhammadu Buhari kasa a ido, ta hanyar shekewa zuwa bangaren siyasar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wata majiya dake kusa da Zango ce ta tabbatar da haka, inda majiyar tace Zango ya yanke shawarar jefar da kwallon mangwaro domin ya huta da kuda ne bayan wata ganawar sirri da yayi da wasu makusanta Atiku Abubakar.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya baiwa jahar Zamfara N60,000,000,000 a matsayin biyan bashi

Siyasa rigar yanci: Adam Zango ya yi fatali da Buhari, ya koma gidan Atiku a guje
Zango Atiku
Asali: Facebook

Zango ya yi wannan ganawa da makusanta Atikun ne da kuma wasu shuwagabanannin jam’iyyar PDP ne a ranar Laraba, 6 ga watan Feburairu a babban birnin tarayya Abuja, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna.

“Zango ya shiga Abuja a ranar Laraba, kuma yayi wata tattaunawa mai muhimmanci da wasu makusanta Atiku Abubakar, da kuma shuwagabannin jam’iyyar PDP, an tattauna batutuwa da dama, inda suka yi masa tayin komawa jam’iyyar PDP, kuma ya amince.

“A yanzu haka Zango na kan hanyarsa ta komawa Kaduna daga Abuja, inda zai shirya taron manema labaru domin bayyana ma Duniya dalilinsa na ficewwa daga APC, tare da janye goyon bayansa ga takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari, da kuma rungumar takarar Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.” Inji shi.

Wannan mataki da Adam Zango ke shirin dauka yayi matukar baiwa jama’a mamaki, musamman wadanda suka san shi a matsayin dan gane kashenin shugaba Buhari, sai dai dama a yan kwanakin nan a jiyo shi yana korafin yadda gwamnatin APC ke yi ma yan fim rikon sakainar kashi.

Ko a ranar Laraba sai da aka hangi Zango yana watsa kamfe da abokinsa, kuma sanannen mai goyon bayan takarar Atiku Abubakar, Zaharaddeen Sani ya buga a shafinsa na kafar sadarwar zamani na Instagram, wanda hakan ke nuna ana tare.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng