Ina shiri da Buhari kuma na san zai kirkiro Jiha a Kasar Inyamurai – Gwamnan Anambra

Ina shiri da Buhari kuma na san zai kirkiro Jiha a Kasar Inyamurai – Gwamnan Anambra

Mun ji labari cewa gwamna Willie Obiano na jihar Anambra ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta kirkiro wata sabuwar jiha a cikin Kudu maso gabashin Najeriya.

Ina shiri da Buhari kuma na san zai kirkiro Jiha a Kasar Inyamurai – Gwamnan Anambra
Gwamnan Jihar Anambra yace Buhari zai kara wata Jiha a kasar Ibo
Asali: Depositphotos

Mai girma gwamna Willie Obiano yayi wannan jawabi ne dazu a lokacin da wasu manyan kasar Ibo a karkashin kungiyar nan ta Ohaneze Ndigbo na reshen jihar Legas su ka kai masa ziyara a fadar sa ta gwamna da ke Amawbia.

A yau Ranar Laraba dinnan ne Mista Willie Obiano yace gwamnatin tarayya ta na da niyyar kara kafa wata jiha a kasar Inyamurai. Gwamnan na APGA yace shugaba Buhari yana da shiri na musamman ga mutanen Ibo da ke kasar nan.

Gwamnan wanda yake wa’adin sa na karshe a kan karagar mulki ya fadawa wadanda su ka kawo masa ziyara cewa shugaban kasar yana da ra’ayin cewa akwai bukatar a kara wata jiha guda a cikin yankin kudu maso gabashin kasar nan.

KU KARANTA: Gwamnan Imo ya nemi Inyamurai su yi wa kan su karatun ta-natsu

Bayan haka kuma gwamna Obiano ya kara da cewa yana sa rai cewa gwamnatin Najeriya wanda shugaban kasa Buhari yake jagoranta za ta tsaida ranar 16 ga watan Nuwamba a matsayin ranar hutu domin a rika tunawa da Nnamdi Azikiwe.

Dr. Nnamdi Azikiwe yana cikin manyan Najeriya da aka yi, kuma shi ne shugaban kasa na farko a tarihin kasar. Obiano yace ba za a taba mantawa da Marigayi Azikiwe a kasar Inyamurai ba don haka yake ganin akwai bukatar a karrama sa.

Kwanaki ne Willie Obiano yayi kaca-kaca da shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo na Najeriya, saboda nuna goyon bayan sa ga Atiku Abubakar inda yake ganin cewa gwamnatin Buhari ta cancanta ta zarce.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel