Zagon kasa: Tambuwal ya salami daya daga cikin kwamishinonin sa

Zagon kasa: Tambuwal ya salami daya daga cikin kwamishinonin sa

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya cire kwaminnan san a yada labarai, Bello Goronyo, bisa zargin sa da yin zagon kasa ga takara da gwamnatin Tambuwal.

A jawabin da Abu Shekara, kakakin gwamnan ya fitar, ya ce Tambuwal ya umarci babban sakatare a ma’aikatar yada labarai da ya cigaba da gudanar da aiyukan ma’aikatar.

Mai girma gwmana Aminu Waziri Tambuwal ya cire Barista Bello Goronyo daga mukamin da ya nada shin a kwamishinn yada labarai.

“Ana umartar babban sakatare a ma’aikatar da ya cigaba da gudanar da aiyukan ma’aikatar ta yada labarai

“An salami kwamishinan daga aiki ne bayan samun sa da laifin yin zagon kasa da cin dunduniyar gwamnati da aiyukan alherin da ta ke yi a jihar Sokoto,” a cewar jawabin Shekara.

Zagon kasa: Tambuwal ya salami daya daga cikin kwamishinonin sa

Tambuwal
Source: Depositphotos

Kafin fitar wannan sanarwa ta cire kwamishinan, Legit.ng ta sanar da ku cewar kwamishanan yada labaran jihar Sokoto, Barista Bello Muhammad Goronyo, ya sauya sheka daga jam'iyyar Peopes Demcratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).

DUBA WANNAN: Kowa ya yi zagi a kasuwa: Ba zan nemi nemi tazarce fiye da sau 2 ba – Buhari

Goronyo ya kasance mai magana da yawun gwamnatin jihar kuma kakakin yakin neman zaben gwamna Aminu Waziri Tambuwal a zaben da za a yi a makonni masu zuwa.

Ya sanar da sauya shekarsa ne a jiya, Talata, a taron kaddamar da yakin neman zaben APC da akayi a garin Wammako, mahaifar jigon jam'iyyar APC na jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wammako.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel