Yadda duniya tayi asarar $200m, bayan mai gadinsu ya mutu bai fadi lambar sirrin ba

Yadda duniya tayi asarar $200m, bayan mai gadinsu ya mutu bai fadi lambar sirrin ba

- Akwai biliyoyin daloli da ake hada-hada dasu na internet, da ake kira bitcoin

- Mutane na son zagaye bankuna da gwamnati wajen harkokin kudinsu

- Ya mutu bai bada password ba, don haka babu wanda zai ci kudin

ASSU strike

ASSU strike
Source: UGC

Masu ajiyar kudi a bankunan Intanet, wadanda ake boyewa don kar gwamnati ko bankuna su sani ko su ci haraji daga ciki, suna cikin jimami a jiya, bayan da wanda ya hada bankin bangaren kasar Canada mai makwabtaka da Amurka yayi mutuwar ba-zata.

Mutuwar tasa ta bagatatan, ta dimautar da masu kudin ajiya har $190m, biliyoyi in aka juya zuwa naira, domin kuwa bai fadi ko bada password din yadda za'a amfana da kudin ko a sayar a bankuna a karba ba.

Cryptocurrency dai, kudi ne da ake hada su a intanet in aka saukaka ko warware wata matsalar kimiyya ko lissafi, wadanda ake kira bitcoin.

GA WANNAN: Kungiyar Kananan hukumomin Najeriya sun zabi wanda suke so ya zama shugaban kasa a Mayu

A shekarar 2017-2018 sai da wannan kudi na bitcoin yayi tashin da ba'a taba gani ba, inda kowacce kwandala daya ta kudin ya kai fin dala $2,000 a kasuwar bankuna ta duniya, kuma mutane masu kudin suka ci kazamar riba.

Hanyoyin kudin cryptocurrency dai, wadanda ake hada wa da ilimin boko, sun zamo wata hanya da masu wayo ke sana'a ko hada-hadarsu ba tare da gwamnati ta sani ba balle ta karbi haraji, kuma ko a nan Najeriya akwai wurare da zaka iya sauya su da tsabar kudi ta dala da Naira.

Bankin Quadriga CX dai a Canada, na can na duba yadda zai iya biyan jama'a kudadensu tun bayar mutuwar Gerald Cotten, CEO dinsu, dan shekara 30 da ya rasu a Disamba a Indiya, bayan 'yar jinya ta Crohn’s disease.

Allah masa rahama, ya fidda kudin kowa ya samu hakkinsa, Amin.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel