Yadda Dikko Inde ya sace N1b a lokacin Jonathan da PDP - ICPC

Yadda Dikko Inde ya sace N1b a lokacin Jonathan da PDP - ICPC

- A sati me zuwa ne ICPC zata gurfanar da tsohon shugaban hukumar custom da kuma wasu mutane guda Biyu bisa tuhumar su da satar kudi sama da N1m.

- Ana tuhumar Mr Dikko da aikata laifuka da dama wanda ya shafi satar kudi

- Wannan laifi ya sabawa doka ta FHC/ABJ/CR/21/2019-FRN zai kuma gurfana a gaban babbar kotu dake birnin tarayya

Yadda Dikko Inde ya sace N1b a lokacin Jonathan da PDP - ICPC

Yadda Dikko Inde ya sace N1b a lokacin Jonathan da PDP - ICPC
Source: UGC

A ranar Alhamis ta sati mai zuwa ICPC zata gurfanar da tsohon shugaban custom Abdullahi Dikko da wasu mutane guda Biyu bisa ga laifin satar kudi wanda yawansu ya haura N1b.

Wannan lamari na Abdullahi Inde Dikko ya sabawa doka ta FHC/ABJ/CR/21/2019-FRN saboda haka zai gurfana a babbar kotun jihar Abuja karkashin alkalancin mai shari'a Lucia Ojukwu.

Ana tuhumar Mr Dikko tare da tsohon mataimakin sa Garba Makarfi da kuma Umar Hussain lauya kuma mamallakin Capital law office da aikata wannan laifi.

Wadanda ake tuhumar sun nemi manajan darakta na Cambial limited Yemi Obadeyi daya biya Capital Law office kudi wanda yakai N1.1b bisa tsaya masa da sukayi.

GA WANNAN: Anyi wa 'yan Kwastam bore a Kano, har da kone-kone

ICPC suna tuhumar Makarfi da Dikko dayin amfani da asusun bankin Hussain wajen karbar kudin yayin da shi kuma Hussaini ya fitar da kudin zuwa wasu asusun da ban a tsakanin 6 ga watan Afrilu shekara ta 2010.

Sannan ana tuhumar Mr Makarfi da karbar kudade wanda suka kai dalar amurka $3m a tsananin watan Afrilu zuwa Disemba 2010.

Mr Dikko ya kasance shugaban custom tun daga watan Agusta 2009 har zuwa 2015 wanda an sameshi da aikata laifuka makamantan hakan da dama.

Dadin dadawa a shekarar data gabata sunan Mr Dikko ya fito a cikin jerin sunayen bayarin gwamnati wanda gwamnatin tarayya ta fitar ta bakin Lai Mohammed.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel