Tabarbarewar ilimin firamare a Kaduna ya saka Farfesa zubar da hawaye

Tabarbarewar ilimin firamare a Kaduna ya saka Farfesa zubar da hawaye

Babban rijistara a hukumar kula da ilimin addinin Islama da harshen larabci (NBAIS), Farfesa Muhammad Shafi’u, ya zubar da hawaye saboda tabarbarewar ilimi a makarantun firamarem gwamnati da ke karamar hukumar Zaria, lamarin da ya sa shi yin kira ga gwamna Nasir El-Rufa’I da ya kawo dauki a bangare.

Farfesa Shafi’u, mai rike da mukamin wakilin makarantar Zazzau, ya yi wannan kira ne yayin wani taron tsofin daliban makarantar firamaren Sarki Ja’afaru da ke kofar Gayan a garin Zaria.

Da ya ke gabatar da jawabi a matsayin san a babban bako a wurin taron tsofin dalliban, Farfesa Shafi’u ya zubar da hawaye a kan yanayin lalacewa da makarantar firamaren ke ciki.

Bai kamata a bar tsohuwar makaranta kamar ta Sarki Ja’afaru, da a shekarar 1942 ta kasance daya daga cikin manyan makarantu uku a garin Zaria, ta lalace ba,” a cewar Farfesa Shafi’u.

Tabarbarewar ilimin firamare a Kaduna ya saka Farfesa zubar da hawaye
Malam Nasir El-Rufa'i
Asali: Depositphotos

Bayan ya yi korafi bias halin ko-in-kula da wasu manya a garin Zaria su ka nuna bias lalacewar makarantar, Farfesa Shafi’u ya dauki alkawarin bayar da gudunmawa domin farfado da makarantar.

DUBA WANNAN: Shigar Atiku Amurka alfarma ce ta wucin gadi - Rahoton Reuters

Kazalika, Aminu Ramalan, wakilin dan majalisar dokoki mai wakiltar Zaria, Abbas Tajudden, ya dauki alkawarin bayar da gudunmawa wajen sake gina makarantar.

A matsayin san a mai kaddamar da littafin hotunan tsofin daliban makarantar, Tajudeen ya sayi littafi guda daya a kan N100,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng