Siyasar Kano: Lokutta 3 da aka kwashi yan kallo tsakanin Shekarau da Kwankwaso

Siyasar Kano: Lokutta 3 da aka kwashi yan kallo tsakanin Shekarau da Kwankwaso

Yayin da babban zaben shekarar 2019 ke karatowa, wani siyasar da zai dauki hankalin mutane shine zaben Sanatan mazabar Kano ta tsakiya, inda za’a fafata tsakanin tsofaffin gwamnonin jahar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Duk da yake ba Kwankwason bane dan takaran jam’iyyar PDP da zai fafata da Malam Ibrahim Shekarau a zaben Sanatan ba, inda jam’iyyar ta tsayar da dan majalisar wakilai, Sani Aliyu Madakin Gini, amma sanin kowa ne Madakin Gini babban dan gaban goshin Sanata Kwankwaso ne.

KU KARANTA; Rundunar soji ta kama 'yan dabar siyasa da muggan makamai, hotuna

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan karawa tsakanin Shekarau da Kwankwaso ne zai zama fafatawa ta hudu da suka buga da juna a siyasar jahar Kano tun bayan dawowar Najeriya bisa turbar Dimukradiyya a shekarar 1998.

Siyasar Kano: Lokutta 3 da aka kwashi yan kallo tsakanin Shekarau da Kwankwaso
Shekarau da Kwankwaso
Asali: Twitter

Arangama ta farko da aka fara samu tsakanin jigogin siyasar biyu ta faru ne a shekarar 2003, shekarar da Shekarau ya tsaya takarar gwamnan jahar Kano a jam’iyyar adawa ta APP, inda ya kayarda gwamnan Kano mai ci, Rabiu Kwankwaso.

Arangama ta biyu kuma ta faru ne a shekarar 2007, a lokacin da Shekarau ke bukatar zarcewa akan kujerar gwamna, inda ya fafata da dan takarar Kwankwaso daga jam’iyyar PDP, Ahmed Garba Bichi, anan ma Kwankwaso ya sha kasa.

Har sai a shekarar 2011 ne Kwankwaso ya samu damar rama biki akan Malam Ibrahim Shekarau, inda ya kayar da dan takararsa, Malam Salihu Sagir Takai a zaben gwamnan jahar Kano, wanda hakan ya baiwa Kwankwaso damar sake zama gwamna a karo na biyu.

Sai dai ba’a sanin maci tuwo sai miya ta kare, domin kuwa zaben 2019 zai iya bada mamaki sakamakon duka tsofaffin gwamnonin biyu suna da karfi a mazabar Kano ta tsakiya, mazabar data kunshi kananan hukumomi goma sha biyar.

Kananan hukumomin sun hada da Nassarawa, Dala, Gwale, Municipal, Tarauni, Kumbotso, Fagge, Gezawa, Minjibir, Dawakin kudu, Warawa, Kura, Garun Malam, Madobi, da Ungogo, inda Shekarau ya fito daga Nassarawa, shi kuwa dan takarar Kwankwaso, Madaki ya fito ne daga Dala.

Alkalumma sun mazabar Kano ta tsakiya nada adadin masu kada kuri’a guda 2,530, 281 a shekarar 2015, kuma Kwankwaso daga jam’iyyar APC ya samu kuri’u 758, 383, yayin da Bashir Lado na PDP ya samu kuri;u 205, 809.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng