Mohammed Abacha ya fara yakin neman zaben Gwamna a Jam'iyyar APDA

Mohammed Abacha ya fara yakin neman zaben Gwamna a Jam'iyyar APDA

- Mohammed Sani Abacha ya kara fitowa takarar Gwamna a Kano

- Yaron Marigayi Janar Abacha yace zai samawa jama’a aikin yi

- Abacha ya dai taba jarraba sa’ar sa a zaben 2011 inda ya sha kasa

Mohammed Abacha ya fara yakin neman zaben Gwamna a Jam'iyyar APDA
Abacha ya sake fitowa takarar Gwamna a Jihar Kano
Asali: Getty Images

Labari ya zo mana cewa yaron marigayi tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya kaddamar da yakin neman takarar sa a zaben 2019. Mohammed Sani Abacha zai nemi kujerar gwamnan Kano ne a karkashin jam’iyyar APDA.

Wannan ne karo na biyu da Mohammed Sani Abacha yake harin kujerar gwamna a Kano, bayan karawar da yayi a 2011 a karkashin jam’iyyar CPC mai adawa kafin a canza sunan sa a matsayin ‘dan takara da Janar Jafaru Isa mai ritaya.

KU KARANTA: ‘Dan takarar Gwamnan Kano yayi wa Buhari alkawarin makudan kuri’u

Alhaji Abacha yana neman takarar gwamna ne wannan karo a jam’iyyar adawar nan ta Advanced Peoples Democratic Alliance (APDA). Abacha yace idan ya samu mulki zai tada masana’antun jihar domin jama’a su samu aikin yi.

Yaron marigayi Sani Abacha ya kuma yi alkawarin cewa zai rage barnar dukiyar da gwamnatin Kano ke yi muddin ya zama gwamna. Shugaban jam’iyyar APDA na kasa, Shitu Mohammed ya nemi jama’a su zabi Abacha a zaben bana.

Jam’iyyar tayi wannan taro na fara shirin yakin neman zabe ne a filin wasa na Polo da ke cikin jihar Kano. Abacha yayi wa jama’an jihar alkawari cewa zai inganta harkar tattali da noma ya kuma maida asabiti da ilmi su zama kyauta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel