Siyasar Kano: Dalilin da ya sa ban halarci mahawarar 'yan takara ba - Ganduje

Siyasar Kano: Dalilin da ya sa ban halarci mahawarar 'yan takara ba - Ganduje

Kwamitin yakin neman sake zaben Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gwamnan Kano ya bayar da dalilan da su ka sa gwamanan bai halarci mahawarar 'yan takarar gwamna da sashen Hausa na BBC y shirya ba a jami'ar Bayero da ke Kano.

Kwamitin ya ce, gwamnan bai samu damar halartar taron ba ne saboda karo da ya yi da jadawalin yakin neman zaben da yake kaddamar wa a kananan hukumomin jihar.

Malam Muhammad Garba, kwamishinan yada labarai kuma sakataren watsa labarai na kwamitin kamfen din Ganduje, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Garba ya bayyana cewa a cikin sati biyu da su ka gabata, gwamna Ganduje ya mayar da hankali ne wajen ganin ya zagaya lungu da sako na jihar Kano domin saduwa da jama'a ta hanyar gudanar da taron kamfen a fadin kananan hukumomi 44 da jihar ke da su.

Siyasar Kano: Dalilin da ya sa ban halarci mahawarar 'yan takara ba - Ganduje
Ganduje
Asali: Depositphotos

A cewar sanarwar, "makasudin yin mahawara shine domin dan takara ya fada wa jama'a irin aiyukan da zai yi ma su idan ya ci zabe. Gwamna Ganduje yana sanar da jama'a irin aiyukan da gwamnatinsa ta yi da kuma wadan da za ta yi idan an zabe ta a wurin taron kamfen din sa.

"Mai girma gwamna ya so halartar wurin mahawarar amma saboda dumbin jama'a na jiran sa a wurin taron yakin neman zabe, sai ya garzaya domin halaratar wurin," kamar yadda ya ke a cikin sanarwar.

DUBA WANNAN: Fusatattun matasa sun kai hari ofishin INEC, sun kona katin zabe ma su yawa

Sanarwar ta cigaba da cewa, jama'a sun isa zama shaida a kan irin aiyukan alheri na raya kasa da al'umma da gwamnan ya yi a jihar Kano.

Kwamishinan ya kara da cewa ragowar 'yan takara da su ka halarci wurin mahawarar sun fadi irin manufofin da su ke son cimma ne idan an zabe su, lamarin da ya ce shine abin da gwamnan ke yi a duk wurin kaddamar da kamfen da ya halarta.

Kazalika, ya kara da cewa idan aka sake zaben ta, gwamnatin Ganduje za ta mayar da hankali ne wajen karasa aiyukan da ta fara da kuma kirkirar wasu sabbi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel