Dogarin Buhari ya bayyana yadda IBB yayi juyin mulki lokacin Idiagbon yana Makkah

Dogarin Buhari ya bayyana yadda IBB yayi juyin mulki lokacin Idiagbon yana Makkah

Kwanakin baya ne Alhaji Mustapha Jokolo wanda shi ne Dogarin Janar Muhammadu Buhari a lokacin yana shugaban kasa a lokacin Soja ya bada labarin juyin mulkin da aka yi wa Shugaba Buhari a 1985.

Dogarin Buhari ya bayyana yadda IBB yayi juyin mulki lokacin Idiagbon yana Makkah
Babangida yayi wa Buhari juyin mulki a shekarar 1985
Asali: Depositphotos

Mustapha Jokolo yayi wannan bayani ne lokacin da shi da wasu mutane du ka kai wa Buhari ziyara a fadar shugaban kasa. Jokole yace an hambarar da gwamnatin Sojan Buhari ne a lokacin Mataimakin sa Janar Tunde Ighiabon ba ya kasar.

A watan Agustan 1985, Jokole yana kasa mai tsarki inda yake aikin Hajji. A wancan lokaci, Sarkin Saudiyya ya nemi Tunde Idiagbon ya tsaya a kasa mai tsarkin a aiko masa iyalin sa a Makkah domin gudun Sojoji su yi ram da shi a gida.

KU KARANTA: Jigawa ta cika makil da jama'a da suka fito tarbar Buhari

Manjo Janar Tunde Idiagbon bai yi na’am da wannan tayi ba inda ya nemi ya koma gida kashegarin ranar da ya samu labarin kifar da gwamnatin su. Idiagbon ya fadawa Sarkin Saudiyya cewa zai koma Najeriya ko da kuwa za a kashe shi.

Jokolo yace mataimakin na shugaba Buhari bai ci amanar sa ba ko a lokacin da ya shiga wani hali, inda ya dawo Najeriya ba tare da jin tsoron sabon shugaban kasa na wancan lokaci Janar Ibrahim Badamasi Babangida zai kama sa ya daure ba.

Tunde Idiagbon wanda asalin sa Mutumin kasar Ilorin ne a cikin jihar Kwara, ya rasu kusan shekaru 20 da su ka wuce. Idiagbon yayi aiki da Buhari bayan kifar da gwamnatin Shagari inda su kayi mulki daga karshen 1983 zuwa shekarar 1985.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng