Kwankwaso yace kofar PDP a bude ta ke ga wadanda su ka koma wajen Ganduje

Kwankwaso yace kofar PDP a bude ta ke ga wadanda su ka koma wajen Ganduje

A jiya da dare ne tsohon gwamnan Rabiu Musa Kwankwaso yayi hira a gidajen rediyon Kano. Tsohon gwamnan ya tattauna ne a kan manyan batutuwan da su ka shafi zaben 2019 yake kusantowa a Najeriya.

Kwankwaso yace kofar PDP a bude ta ke ga wadanda su ka koma wajen Ganduje

Buhari yayi babban kuskure na daga hannun Ganduje a Kano – inji Kwankwaso
Source: Twitter

Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kuskure mai girma na fadawa Duniya cewa a sake zaben gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda ake zargi da karbar rashawa na makudan Daloli.

Kwankwaso wanda ya nemi takarar shugaban kasa a PDP inda ya sha kashi wajen zaben fitar da gwani ya bayyana cewa ko kadan ba zai ki Abba Yusuf ya nada ni cikin masu ba sa shawara idan ya zama Gwamna a zaben 2019 ba.

Injiniya Kwankwaso yace ba aibu bane don ya zama mai ba gwamnan Kano shawara a kan harkar ilmi ko aikin ruwa domin a nan ne ya samu kwarewa. Kwankwaso ya kuma ce dole a maida hankali kan ilmi domin fetur ya kusa daina rana.

KU KARANTA: Atiku Abubakar ya kaddamar da yakin zabe a jihar Abia cikin salo

Abba Yusuf wanda shi ne ‘dan takarar gwamna a PDP ya samu tikiti ne a dalilin Rabiu Kwankwaso, wanda hakan ya sa wasu manyan ‘yan kwankwasiyya su ka koma APC, bayan sun rasa tikitin gwamna a karkashin jam’iyyar adawar.

Tsohon gwamna Kwankwaso yace bai ki gobe wadanda su ka sauya-sheka su dawo a cigaba da tafiya a jam’iyyar PDP ba. Sanatan na Kano yace dama can wadannan manyan ‘yan siyasa sun koma APC ne saboda hana su takara a PDP.

Haka kuma Kwankwaso ya ce PDP za ta ci zabe inda yace ba sai ma ya daga kafar wandon sa wajen yakin neman zabe ba domin rigar gwamna mai-ci za ta sa ya sha kasa a zaben da za a yi saboda zargin karbar rashawar da ke kan sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel