Ashe da gaske ne, camfin nan na satar banten mata yayi kamari a kudu, an kamo 19

Ashe da gaske ne, camfin nan na satar banten mata yayi kamari a kudu, an kamo 19

- Jami'an hukumar yaki da rashawa sun damke wasu yan damfarar yanar gizo

- Mutanen sun kware a damfarar mutane su samu kudi ta hakan ko ta soyayya

- A gurin kamen ana samu wayoyi, motoci na alfarma da kayayyakin sihiri

Ashe da gaske ne, camfin nan na satar banten mata yayi kamari a kudu, an kamo 19

Ashe da gaske ne, camfin nan na satar banten mata yayi kamari a kudu, an kamo 19
Source: Facebook

Jami'an hukumar yaki da rashawa ofishin yankin Ibadan sun kama mutane 19 da ake zargi da damfara ta yanar gizo a yankin Ologuneru na birnin Ibadan da Akobo, jihar Oyo.

Mutanen sune, Bamidele Ayodele Samson, Bamidele Philip, Tunji Oladapo Sowale, Bolalaji Olalekan da kuma Abdulrauf Abiodun.

Ashe da gaske ne, camfin nan na satar banten mata yayi kamari a kudu, an kamo 19

Ashe da gaske ne, camfin nan na satar banten mata yayi kamari a kudu, an kamo 19
Source: Facebook

Sauran sun hada da Olaleye Pelumi, Anuokuwapo Olanrewaju, Paul Damilola, Olateye David Tobi, Arewa Adekunle Ibrahim, Oyesanmi Ayomikun Oluwaseun, Olaleye Israel, Adediran Kemisola, Omobolade Alarape da Olowolusi Oluwatomisin.

An kama sauran mutane hudun da ake zargi da safiyar juma'a 1 ga watan Fabrairu 2019 a maboyar su dake Akobo, Ibadan.

A wani samame da shugaban ofishin na yankin, Friday Ebelo, ya jagoranta, wadanda ake zargin masu shekaru tsakanin 21 zuwa 35 sun sha mamakin kamen da akayi musu a wani gurin buyar su.

5 daga cikin su sunce daliban jami'a ne sai kuma goma daga daga cikin su sunce suna su suka dau kansu aiki a wurare daban daban.

A halin yanzu suna taimakon jami'an da bayanai masu amfani.

GA WANNAN: Ai ko don kunyar iyali na na karasa gadar gabashin Najeriya ta 2nd Niger Bridge - Atiku

Ofishin sun samu alkiblar kamen ne ta hanyar rahoton sirri, in da suka samu cewa matasan na aiyukan damfara kama daga turo sakonnin bogi don samun kudi daga mazauna USA, soyayyar karya ta shafukan soyayya na yanar gizo da sauran su.

A inda aka kama su, an samu motoci sabbin fitowa na alfarma guda hudu, laptop 5, wayoyi 20 a ciki akwai iPhone 10 sai karamar jaka mai kunshe da kayayyakin sihiri. Takardu da yawa da suka hada da Fasfotin fita kasashen waje da katin cire kudi a banki.

A wani cigaba dangane da hakan, jami'an sun damko mutane hudu a maboyar su a ranar juma'a a Akobo, Ibadan. Yan damafarar yanar gizon na da shekaru 21 zuwa 30.

Kama su ya biyo bayan rahoton sirri da hukumar ta samu akan damfarar da suka shahara.

A lokacin da aka kama su, an samu layikan waya, mota daya ta alfarma, laptops, wayoyi, kayan sakawa a ciki na mata da jakunkuna hudu na kayayyakin sihiri.

An samu takardun bogi a tare da wadanda ake zargin.

Nan ba da jimawa ba za a gurfanar dasu a gaban kotu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel