Zamu yi qasa-qasa da magudin Saraki a siyasar Kwara a wannan karon - Gwamnatin Tarayya

Zamu yi qasa-qasa da magudin Saraki a siyasar Kwara a wannan karon - Gwamnatin Tarayya

- Saraki da danginsa sun mamaye siyasar jiharsu ta Kwara

- Gwamnati tace zata yi kasa-kasa dashi a wannan karon

- Su Saraki sun koma PDP sunce APC azzaluma ce

Zamu yi qasa-qasa da magudin Saraki a siyasar Kwara a wannan karon - Gwamnatin Tarayya
Zamu yi qasa-qasa da magudin Saraki a siyasar Kwara a wannan karon - Gwamnatin Tarayya
Asali: UGC

A yau ne gwamnatin Tarayya tayi wa jama'ar Kwara alkawarin lasa-lasa da 'siyasar magudi' da wai danniya da Bukola Saraki ke yi a jihar tun 2002.

Zamu yi qasa-qasa da magudin Saraki a siyasar Kwara a wannan karon - Gwamnatin Tarayya
Zamu yi qasa-qasa da magudin Saraki a siyasar Kwara a wannan karon - Gwamnatin Tarayya
Asali: UGC

A cewar gwamnatin dai, shekaru aru-aru Bukola Saraki na amfani da 'yan daba da 'yan fashi wajen yin magudi, danniya da fin karfin jama'a a jihar, lamari da a cewar gwamnatin, ya sanya kowa na tsoronsa ake zabarsa ta dole.

Zamu yi qasa-qasa da magudin Saraki a siyasar Kwara a wannan karon - Gwamnatin Tarayya
Zamu yi qasa-qasa da magudin Saraki a siyasar Kwara a wannan karon - Gwamnatin Tarayya
Asali: Facebook

Lai Muhammed, wanda shima daga jihar ya fito, shi yake wannan bayani, a lokacin da yake kaddamar da sabbin ofisoshin jam'iyyarsa ta APC da ma motocin kamfe a lokacin gangamin jam'iyyar a dazu a birnin Ilorin.

GA WANNAN: Wata biyu za'a hau jirgin kasa kyauta a Najeriya, inji Osinbajo, ana gab da zabe

An dade ana damawa da Bukola da ma ubansa Olusola Saraki a jihar, kai harma da kanwarsa wadda ta nemi gwamna a 2011 amma Abdulfattahi da Sarakin ya kawo ya kayar da ita, duk da mahaifinsu marigayi Olusola bai so ba.

A yanzu dai Saraki shine na uku a matsayi a Najeriya a gwamnatance, kuma ya koma PDP da kujerarsa ta Sanata, sannan kuma gwamna Ahmed ma ya koma PDPn.

Kokarin APC shine lallai ayi maza-maza a dawo da Sanatan gida, inda zai zamo sifiliyan kamar kowa, don ya ffuskanci zarge-zargen amfani da 'yan daba, musamman wadanda suka yi fashi a Offa suka kashe mutane, suka kuma ce wwai su yaransa ne.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel