Kwankwaso ya wakilci Atiku yayin bikin kaddamar da littafi a garin Abuja

Kwankwaso ya wakilci Atiku yayin bikin kaddamar da littafi a garin Abuja

A jiya Juma'a 1 ga watan Fabrairu, tsohon gwamnan jihar Kano kuma wakilin shiyyar Kano ta Tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya wakilci tsohon mataimakin shugaban kasa a wani babban taro da aka gudanar cikin garin Abuja.

Kwankwaso ya wakilci Atiku yayin bikin kaddamar da littafi a garin Abuja
Kwankwaso ya wakilci Atiku yayin bikin kaddamar da littafi a garin Abuja
Asali: Twitter

Mun samu cewa, tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanatan shiyyar Kano ta Tsakiya, Rabi'u Kwankwaso, ya wakilci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a wani babban taro na bikin kaddamar da littafi da aka gudanar cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Kwankwaso ya wakilci dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP yayin bikin kaddamar da wani littafi mai taken 'Politics as Dashed Hopes in Nigeria', wanda Dakta Auwalu Anwar ya wallafa.

KARANTA KUMA: Yakin Zabe: Atiku ya girgiza magoya baya a jihar Enugu da Ebonyi

Taron wanda aka gudanar a cibiyar taro ta 'Yar adua da ke garin Abuja ya samu halarcin tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo da ya kasance uban taro yayin bikin kaddamar da littafin da aka wallafa kan makomar Najeriya a siyasance.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a jiya ne dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya girgiza magoya bayan yayin da ya gudanar ta taron sa na yakin neman zaben sa a jihar Enugu da kuma Ebonyi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel