2019: Dalilan da yasa yankin Yarabawa baza su yi Atiku ba

2019: Dalilan da yasa yankin Yarabawa baza su yi Atiku ba

- Shin wane dan takara yankin kudu maso yamma zata zaba?

- A cikin shekaru 16 an nunawa yankin halin ko in kula

- A wannan mulkin ne of tasan anayi da ita ta hanyar mata aiyukan cigaba da kuma mukaman siyasa

2019: Dalilan da yasa yankin Yarabawa baza su yi Atiku ba

2019: Dalilan da yasa yankin Yarabawa baza su yi Atiku ba
Source: Facebook

A yayin da zaben watan Fabrairu na shugabancin kasa ke kusantowa, babbar tambaya itace yankin kudu maso yamma me suka karu dashi idan har suka zabi daya daga cikin sanannun yan takarar na Jam'iyyar APC da PDP.

Wannan itace tambayar da masu bincike keyi tare da mika abinda suka samo don kintatar abinda ake tsammani a zaben yankin.

Daya daga cikin abinda ya taka rawar gani wajen sa PDP ta fita ran yan yankin shine yanda jam'iyyar ta dau mutanen yankin a lokacin mulkin Jonathan na 2009 zuwa 2015. Mutanen yankin sun yarda kuma sun gani cewa an rufe babin su bangaren kammala aiyukan more rayuwa da kuma zabarsu a mukaman siyasa.

Da wuya mutum ya nuna aiki daya da gwamnatin Goodluck ta fara kuma ta kammala ko kuma wacce Olusegun Obasanjo ya fara sai gwamnatin ta karasa.

Da yawan irin wadannan aiyukan gwamnatin shugaba Buhari ce ta kammala ko kuma suna gab da kamala.

A misali, babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, titin Ibadan zuwa Oyo zuwa Ogbomosho wanda gwamnatin Olusegun Obasanjo ta watangarar a Oyo wanda hakan yasa bangaren Oyo zuwa Ogbomosho ya zamo ba kammalalle ba har tsawon shekaru 16.

Gwamnatin shugaba Buhari ce ke ta gwagwarmayar ganin aikin ya kammala.

GA WANNAN: Majalisin Alkalan kasar nan (NJC) kawai ya sallami Onnoghen - Falana

Wani babban aikin da ya faranta ran yarbawa shine titunan jiragen kasa da ya hada Legas da Ibadan, babban birnin siyasar kudu maso yamma. An fara aikin ne tun lokacin Jonathan amma aka watangarar dashi har sai lokacin Buhari. A halin yanzu anci karfin aikin kuma yana sauri.

Ka gwada tafiya daga Legas zuwa Ibadan wacce zata ci mintuna talatin kacal. Akan mene kudu maso yamma zata zabi nunawa wata jam'iyyar godiyar ta bayan APC ta girmama yankin?

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel