Bayan an gano gwamnonin Nijar a taron APC a Kano, Ribadu ya maida martani

Bayan an gano gwamnonin Nijar a taron APC a Kano, Ribadu ya maida martani

- An gano gwamnonin Jamhuriyar Nijar a Kano da Buhari

- PDP tace dama da 'yan Nijar APC take cuwa-cuwar zabe

- Ribadu ya wanke Ganduje tsaff

Bayan an gano gwamnonin Nijar a taron APC a Kano, Ribadu ya maida martani
Bayan an gano gwamnonin Nijar a taron APC a Kano, Ribadu ya maida martani
Asali: Twitter

Nuhu Ribadu, tsohon shugaban EFCC kuma dodon barayin gwamnati aqq wancan zamani na PDP, ya sanya soso da sabulu ya wanke Ganduje tsaf, kan batun wai laifi ne ya gayyato 'yan APC daga wata kasa suzo taron APC a Kano.

An dai gano gwamnan Damagaram Zinder daga kasar Nijar sun saka kayan APC sun hau mumbarin APC a ziyarar da Buhari ya kai Kano a shekaranjiya Alhamis.

PDP dai ta kira hukumomi da ma INEC da ta dauki mataki, musamman ganin masu gudun hijira 'yan Najeriya dake Nijar ma ance zasu yi zabe a can, lamari da PDPn ke ganin hanya ce ta baiwa bakin haure damar su dangwalawa Buhari kuri'u.

GA WANNAN: Gwamnati ta kwace wata marainiyar N1.05b wadda uwarta ta gudu ta barta

A cewar Nuhu Ribadu dai, babu laifi idan an tabbatar ba zabe suka zo yi ba, a'a, sun dai kawai shigo Kano ne domin taya makwabciyar kasar su murnar shiga zabe lafiya, ganin duk yankin yammacin Afirka na ECOWAS ya bada damar zagawa.

Ribadu yace: Babu dalilin tada jijiyar wuya da PDP take yi, domin kuwa kawai nuna wa duniya bakin suke, sunyi amanna da irin salon mulkin APC da Buhari, musamman a kan batun tsaro da tattalin arziki.

A doka dai, babu dalilin da wasu daga wata kasa zasu shigo Najeriya suyi rawar kadi da wata jam'iyya, sai dai Najeriya da Nijar, kafin zuwan Turawa duk mutane daya ne, masu al'adu da addini daya, kuma basu taba ganin banbancin juna ba don wani layi da aka shata daga Ingila.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel