Lalata fostocin APC: An kama mutane 5 a jihar Kano

Lalata fostocin APC: An kama mutane 5 a jihar Kano

- An kama gurfanar da wasu mutane biyar a gaban kotu bisa zarginsu da lalata fostocin yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Abdullahi Ganduje a jihar Kano

- Wadanda ake zargin sun hada da Abubakar Halliru, Bala Baffa, Tijjani Ali Rugu-Rugu, Sani Asabe da Bala Faska

- Bayan karanto zargin da ake musu, Alkalin kotu ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 7 ga watan Fabrairu

Lalata fostocin APC: An kama mutane 5 a jihar Kano

Lalata fostocin APC: An kama mutane 5 a jihar Kano
Source: Twitter

An gurfanar da mutane biyar a gaban kotun Majistare da ke jihar Kano inda ake zarginsu da lalata fostoci da allunan zabe na jam'iyyar All Progressive Congress (APC) da ke mulki a jihar.

An zarginsu da aikata laifin hadin baki, shirya makirci da tayar da zaune tsaye wanda hakan ya ci karo da sashi na 97, 114 da 327 na dokar Penal Code a jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Ganduje: Kotun Shari'a tayi watsi da karar da aka shigar a kan Jaafar Jaafar

Kamar yadda rahoton rundunar 'yan sanda ya nuna, Wani Abubakar Halliru na kauyen Tarai da ke karamar hukumar Kibiya na jihar Kano ya hada baki da Bala Baffa, Tijjani Ali Rugu-Rugu, Sani Asabe da Bala Faska duk da ke zaune a karamar hukumar Tudun Wada a Kano domin lalata fostocin yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari da na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da niyyar tayar da zaune tsaye.

Alkalin Kotun, Cif Majistare Ibrahim Khalil Mahmood ya dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 7 ga watan Fabrairun shekarar 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel